Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Jigawa Ce Ta Ɗaya Wajen Yin Kasafin Kuɗi A Bayyane A 2022

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙara samun nasarar zama ta ɗaya a bincike kan yin kasafin kuɗi a bayyane a shekarar 2022.

Babban Daraktan Cibiyar Bincike kan Tattalin Arziƙin Al’umma da Samar da Ci Gaba, Tijjani Abdulkareem ne ya bayyana hakan yau Talata a Kano, a taron Arewa maso Yamma na bayyana rahoton binciken Yin Kasafin Kuɗi a Bayyane na Jihohi a 2022.

Tijjani Abdulkarim ya bayyana cewa, dalilin samar da rahoton shine domin a fito da ɓangarorin da suke buƙatar gyararraki, da kuma yanda za a yi aiki tare tsakanin gwamnati da al’umma domin tabbatar da abubuwa na tafiya yanda ya kamata.

Tun bayan shawarwarin ƙungiyoyin ci gaban al’umma na 2015 ne dai, jihohi suke fitar da rahoton kasafin kuɗi domin bayar da dama ga al’umma su fahimci inda aka dosa.

Tijjani ya ce, a binciken da aka gudanar a shekarar 2022, an duba abubuwan da suka shafi yin kasafi a buɗe, bibiyar kasafi, da kuma damar al’umma na sanin abun da ke faruwa game da kasafin da gwamnati ta yi.

A wannan ɓangare, ya yabawa gwamnatin Jihar Jigawa da ta gabata ta Muhammad Badaru Abubakar kan irin wannan jagorancin na tabbatar da cewar an shigar da ƴan jiha wajen yin kasafin kuɗi da bibiyarsa da kuma samar da bayanai a yanar gizo na kasafin kuɗin.

Jihar Kano ce ta ke biyewa Jigawa a matsayin ta biyu, inda ta samu yabo ita ma, yayinda rahoton ya bayyana wasu jihohi da ada suke a kurar baya amma yanzu su ma yunƙuro.