Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

JIGAWA: Garko Ta Haɗejia Na Cikin Damuwa, Ɗaruruwan Almajirai Da Iyalai Sun Rasa Matsugunnai Sakamakon Mamakon Ruwan Sama

Mazauna unguwar Garko, kusa da ramin ruwa na Garko a ƙaramar hukumar Hadejia, Jihar Jigawa, sun fitar da kiran gaggawa ga dukkan matakan gwamnati da su je su ceto al’ummarsu.

Alhaji Isyaku, wakilin mazauna yankin, ya bayyanawa TIMES NIGERIA cewa, ɗaruruwan jama’a, ciki har da almajirai a makarantar Tsangaya dake bakin rafin, sun rasa matsugunnai sakamakon ambaliyar ruwan sama da ta cika yankin.

Ya ce, “Wannan ba sabon lamari ba ne; tun shekarun baya unguwarmu na fama da irin wannan ambaliya amma ba mu samu wani taimako daga ƙaramar hukuma, jiha ko tarayya ba.”

Sun roƙi Gwamna Umar Namadi da cewa “ka zo ka gani da idanunka” domin ganin tsananin halin da suke ciki da kansa.

Mazauna yankin sun tambayi wakilansu da suka yi shiru kan ibtila’in da cewa: “Ina Sanatanmu yake? Ina ɗan majalisar wakilai na tarayya yake? Ina ɗan majalisar dokoki ta jiha yake? Ina shugaban ƙaramar hukuma yake?”

A yanzu dai za a iya cewa, shugabanni sun yi shiru yayin da iyalai ke gudun hijira, yara ba su da mafaka, makarantu sun nutse cikin ruwa kuma hanyoyin samun abin dogaro da kai suna rugujewa.

Wannan ta sa mutanen yankin roƙon ɗaukin gaggawa da cewa “Ba za mu iya ci gaba da rayuwa cikin wannan halin bala’in ba,” tare da jaddada buƙatar agaji nan take daga dukkan matakan gwamnati.