Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Jigawa Golden Stars Ta Koka Kan Zalunci Da Wulaƙancin Da Ta Fuskanta Yayin Karawa Da Barau FC A Kazaure

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars FC ta kai koken hukuncin rashin adalci da cin zarafi da barazana ga ƴan wasan da jami’anta suka fuskanta yayin da suka kara da Barau FC ta Kano, a wasan da aka buga a ranar Asabar, 3 ga watan Mayu, 2025 a filin wasa na Kazaure Township Stadium.

A cikin wasiƙar koke da Ibrahim Isyaku, jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar ya fitar a yau Lahadi, ya bayyana cewa “wasan ya kasance cike da son kai da gazawar haƙiƙanin dokokin ƙwallo wanda hakan ya jefa lafiyar ƴan wasa, jami’ai da magoya baya cikin haɗari.”

Daga cikin abubuwan da kungiyar tai zargi akwai hana su bugun fanareti guda biyu da suka cancanta, fitar da jan kati ga Musa Musa ba tare da wata hujja ba, da kuma amincewa da ƙwallaye biyu da aka ci ta hanyar karya doka.

WANI LABARIN:

Hakazalika, ƙungiyar ta ce Barau FC ta haɗa magoya bayanta waɗanda suka mamaye filin wasa suna zagin ƴan wasan Golden Stars da jami’ansu, tare da kawo wasu da suka yi iƙirarin cewa su jami’an tsaro don su jefa ƙungiyar cikin tsoro da damuwa, wanda daga baya suka samu nasarar hakan.

“Muna da hujjoji da suka haɗa da bidiyon wasan, hotuna na wasu da ba jami’an tsaro ba da shaidun da suka gani da ido,” in ji Isyaku.

Ƙungiyar ta buƙaci hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta gudanar da bincike, da ɗaukar matakin ladabtarwa, tare da ɗaukar matakan tsaro don kauce wa faruwar irin haka a gaba.

Jigawa Golden Stars ta ce “fatanmu shine a kare mutuncin wasan ƙwallo a Najeriya, a kuma tabbatar da adalci da gaskiya domin ci gaban wasan.”