Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

JIGAWA: Jihar Ta Mayar Da Sama Da Naira Miliyan 31 Ga Mahajjata 930 Bayan Samun Ragin Kuɗin Hadaya

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta mayar da fiye da Naira miliyan 31 ga mahajjata 930 da suka yi aikin Hajjin 2025, bayan rangwamen da Masarautar Saudiyya ta yi kan farashin dabbobin hadaya.

Babban Daraktan Hukumar, Ahmed Umar Labbo, ya bayyana hakan ne a Dutse lokacin da Amirul Hajji kuma Sarkin Kazaure, Alhaji Najib Hussaini Adamu, ya miƙa rahoton Hajji na 2025 ga Gwamna Umar Namadi.

Ya ce tattaunawar kai tsaye tsakanin Hukumar da kamfanin Hadaya na Saudiyya ce ta samar da rangwamen, inda “kowane mahajjaci da ya bi ta Hukuma zai karbi naira 42,996,” a cewarsa.

Amirul Hajjin ya ƙara da cewa an mayar da sama da naira miliyan 24 zuwa baitul-malin jiha daga kuɗaɗen aikin da ba a kashe ba, yana danganta nasarar da nuna “gaskiya, bin ƙa’ida da kyakkyawan tsarin sarrafa kuɗi.”

Ya yaba da inganta tsarin abinci, masauki, kula da lafiya da “sabon tsarin ware gidaje tun kafin isowar mahajjata Makkah da rage matsalar ɓatan alhazai.”

Ya ce ba a samu ko ɗaya da ya ɓace ko ta haihu a lokacin aikin ba, “kuma kyautar Sallah ta Riyal 100 daga Gwamna ta farantawa alhazan rai.”

A nasa jawabin, Gwamna Namadi ya gode wa kwamitin Hajjin, yayin da Labbo ya danganta nasarar ga ƙoƙarin gwamnan da yin addu’ar Allah ya ci gaba da jagorantar gwamnan wajen jagorantar jihar.