Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da samar da kayan tallafin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur, biyawa ɗaliban jihar kuɗin karatu a jami’o’i da kuma siyo taraktocin noma guda 54 domin manoman jihar.
Gwamnatin ta amince da aiwatar da waɗannan aiyuka ne a jiya Laraba, yayin gudanar da zaman Majalissar Zartarwar Jihar Jigawa da ya gudana ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar, Malam Umar Namadi.
Sanarwar bayan taron da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Sagir Musa Ahmad ya fitar ta nuna cewar, gwamnatin ta amince da siyo tirela saba’in ta shinkafa, kimanin buhu dubu 42,000, domin rabawa ƴan jihar.
KARANTA WANNAN: Gwamna Namadi Ya Naɗa Masu Ba Shi Shawara Na Musamman Guda 35
Ƙari a kan hakan, gwamnatin ta amince da siyo buhun gero 32,400 (tirela 54), da katan ɗin taliya dubu ɗaya domin rabawa a matsayin tallafin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi.
Sagir Musa ya bayyana cewar za a raba waɗannan kayayyaki ne ƙarƙashin kulawar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar, SEMA, sannan ya ce, adadin kuɗaɗen da za kashe domin siyo waɗannan kayayyaki ya kai naira biliyan uku da miliyan ɗari takwas da dubu arba’in da takwas (N3,848,000,000.00).
Biya Wa Ɗalibai Kuɗin Makaranta
Haka kuma, a zaman Majalissar Zartarwar, gwamnatin Jihar Jigawan ta amince da biya wa ɗaliban jihar da ke karatu a Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutse, FUD; Jami’ar Bayero da ke Kano, BUK; Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, KUST; da kuma Jami’ar Maiduguri, UNIMAID.
A kan wannan, gwamnatin ta ware naira miliyan ɗari da sittin da bakwai, da dubu ashirin da huɗu da ɗari tara da hamsin (N167,024,950.00).
Gwamnatin ta bayyana cewar ta yi hakan ne domin ragewa iyaye nauyin biyan kuɗaɗen karatun da su ke biya wa ƴaƴansu duba da yanayin da ake ciki.
Siyo Taraktoci 54 Don Manoma
Majalissar Zartarwar ta Jihar Jigawa ta kuma amince da siyo taraktocin noma guda 54 a kan kuɗi naira biliyan 1.
Gwamnati za ta siyo waɗannan taraktoci ne ta hannun Kamfanin Siye da Siyarwar Kayan Aikin Gona ta Jiha, JASCO.