Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Jigawa Zata Gabatar Da Ƙwarya-Ƙwaryar Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 44.7

Majalissar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da miƙa ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi na naira biliyan 44,700,000,000 ga Majalissar Dokoki ta jihar domin amincewa.

Majalissar ta amince da miƙa kasafin kuɗin ne a yau, lokacin gabatar da Zaman Majalissar Zartarwa na Jihar karo na uku wanda gwamnan jihar, Malam Umar Namadi ya jagoranta a yau Laraba.

Malam Garba Al-Hadejawi, Mai Temakawa Gwaman Jigawa kan Kafafen Yaɗa Sadarwa na Zamani ne ya bayyanawa TASKAR YANCI sakamakon zaman majalissar zartarwar.

Ya ce, Majalissar ta bayyana buƙatar gabatar da ƙarin kasafin ne saboda ƙarin kuɗaɗe da jihohi suke samu daga kason Gwamnatin Tarayya wanda ya samo asali daga cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi.

KARANTA WANNAN: An Saka Ranaku, Gurare Da Lokutan Tantance Ƴan J-Teach Masu Digiri A Jigawa

Ya ƙara da cewa, gwamnatin ta bayyana cewar, za ta miƙa ƙarin kasafin kuɗin ne domin ta faɗaɗa aiyukan raya ƙasa a fannin ilimi, lafiya, aiyukan raya karkara da kuma gina ɗan’adam.

Majalissar ta kuma alaƙanta buƙatar yin aiyukan saboda matsalolin rayuwar da cire tallafin mai da kuma zubewar darajar naira ya jawo wa al’umma.

Haka kuma a zaman na yau, majalissar ta amince kashe kuɗi naira miliyan 192.68 domin ƙarasa aiyukan magudanan ruwa na garin Kafin Hausa da kuma ƙarasa aiyukan gadojin da ambaliyar ruwa ta lalata a jihar.