Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Jihar Jigawa Zata Kashe Biliyoyi Wajen Gyaran Makarantu Da Siyan Injinan Noma

Majalissar Zartarwa ta Jihar Jigawa, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi, ta amince da aiwatar da wasu ayyuka a taron da ta yi ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba, 2024.

Majalissar ta amince da bayar da kwangilar fiye da naira biliyan 2.5 don ginawa, gyarawa da tsaftace makarantun firamare da na sakandare a dukkan ƙananan hukumomi 27 na jihar.

Haka kuma, ta amince da bayar da kwangilar sama da naira biliyan 1 don gyaran makarantun da guguwar iska ta lalata sannan kuma an rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa cibiyar daliban ICAN a Dutse.

Haka kuma, an amince da ware fiye da Naira biliyan 26 don sayen kayan aikin noma, wadanda suka hada da tarakta 300 da sauran injina daban-daban, tare da ware naira miliyan 263 don horar da mutane 30 aikin gyaran injinan a kasar Sin.

Majalissar ta kuma amince da fitar da naira biliyan 8.19 don biyan kaso 30 cikin 100 na kudin sayen kayayyakin da aikin horar da mutane.

Ana sa ran, wadannan aiyuka zasu taimaka wajen bunkasa ilimi da noma, samar da ayyukan yi, da kuma cigaban jihar Jigawa mai ɗorewa.