Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Jihohi Da Yankunan Da Sabbin Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya Da Za A Naɗa Zasu Fito

Gwamnatin Tarayya ta fara aikin naɗa sabbin manyan sakatarori biyar, uku daga cikinsu za su jagoranci sababbin ma’aikatun da aka samar.

Wata wasiƙa daga Ofishin Shugaban Ma’aikata ta bayyana cewa wannan dama ce ga manyan daraktoci da ke matakin GL 17 da suka cika sharuɗɗan cancanta.

Shugaban Ma’aikata, Didi Walson-Jack, ya ce, “Za a cike guraben jihohin Imo da Babban Birnin Tarayya, da kuma sabbin kujeru uku na yanki da aka ware bisa tsarin karɓa-karɓa na yanki.”

Sharuɗɗan sun haɗa da kasancewa ma’aikaci mai tabbatacciyar rajista a IPPIS, shekaru biyu a matsayin Darakta, da rashin kusantar ritaya kafin 31 ga Disamba 2026.

Mata ba za su iya amfani da asalin jihar mijinsu wajen nuna asalin jiharsu ba, sai dai jihohin da suka fito.

Shugaban Ma’aikata ya buƙaci a tabbatar babu shari’ar ladabtarwa a kan kowanne mai neman muƙamin.

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya riga ya nada aƙalla sakatarori 26 tun hawansa karagar mulki.