Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Jure Ƙishi Ba Juriya Ba Ce Gangancin Jefa Kai Cikin Matsalar Ƙoda Ne

Daga: Sama’ila Bature Jahun

Masana kiwon lafiyar ƙoda sun bayar da shawarar shan tsabtataccen ruwa aƙalla lita 2 zuwa 3 a kowace rana. Wato lita 2 (pure water 4) zuwa 3 (pure water 6) shi ne mafi ƙarancin ruwan da mutum ya kamata ya sha a rana. Saboda haka, shan ruwa fiye da lita 2 zuwa 3 ƙarin alfanu ne ga lafiyar ƙoda musamman a wannan lokaci na zafi.

Shan isasshen ruwa na taimaka wa aikin ƙoda wajen wanke ko tace jini da ruwan jiki daga guba da sauran muggan sinadarai da jiki ke samarwa domin fitar da su zuwa cikin fitsari.

Bugu da ƙari, yawan fitar gumi na nuni da yawan ruwan da ke fita daga jiki. Kuma yawan gumin da ya fita na nuni da ƙarancin fistarin da za a samu.

Saboda haka, ƙaranta shan ruwa na da haɗarin gaske domin yana haifar da dunƙulewar sinadaran da ke cikin fitsari har daga ƙarshe ya haifar da tsakuwar ƙoda. Ciwon tsakuwar ƙoda na iya tilasta yin tiyatar ƙoda domin cire tsakuwar.

Ruwa Rayuwa Ne!