Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

JUYIN MULKI: Sojoji Zasu Kare Demokaraɗiyyar Najeriya Komai Matsalolinta – Shugaban Sojoji

Hafsan Hafsoshin Najeriya, Lieutenant General Taoreed Lagbaja, a jiya Asabar ya yi alƙawarin cewa, sojojin Najeriya zasu ci gaba da kare demokaraɗiyyar Najeriya komai matsalolin da take fuskanta.

Janar Lagbaja ya bayar da wannan tabbacin ne, lokacin da yake jawabi a bikin faretin yaye jami’an kwas ɗin Executive Commission na Ɗaya wanda aka gudanar a Army School of Infantry da ke Jaji, a Jihar Kaduna.

Ya ce, buƙatar kowanne ɗan Najeriya ita ce, ingantacciya kuma ɗorarriyar demokaraɗiyya wadda ke amfani da kundin tsarin mulki, wadda kuma take kare martabar duk wani ɗan ƙasa na-gari.

Ya kuma gargaɗi jami’an sojojin da su guji duk wani abu da zai kai ga cin amanar ƙasa, inda ya jaddada cewar su guji shiga siyasa wajen aiwatar da aiyukansu.

Lagbaja dai na yin waɗannan maganganu ne a daidai lokacin da tunanin yiwuwar juyin mulki a Najeriya ke yawo a zuƙatan ƴan ƙasa, ganin abin da ya faru da Jamhuriyar Nijar.

Mako biyu da suka gabata ne dai, sojojin Nijar suka kifar da gwamnatin demokaraɗiyyar ƙasar a wani juyin mulki da suka yi.