Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

JUYIN MULKIN NIJAR: Ƴan Arewa Na Asarar Naira Biliyan 13 Duk Sati

Ƴan kasuwa a yankin Arewacin Najeriya sun koka kan yanda suke asarar kimanin naira biliyan 13 duk sati saboda rufe boda da aka yi biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar.

A ranar 4 ga watan nan na Agusta ne, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin rufe bodojin tsakanin Najeriya da Nijar a matsayin wani mataki na nuna rashin amincewarsa da juyin mulkin da aka yi.

Bodojin da aka rufe sun haɗa da ta Jibiya da ke Jihar Katsina, ta Illelah da ke Jihar Sokoto da kuma ta Maigatari da ke Jihar Jigawa.

Shugaban Ƙungiyar Bunƙasa Arziƙin Arewa, Ibrahim Yahaya Dandakata ne ya bayyana asarar da ƴan kasuwar Arewan suke yi a dalilin rufe bodar.

KARANTA WANNAN: Ka Gaggauta Ceton Miliyoyin Mutane Daga Matsananciyar Yunwa – Dattawan Arewa Ga Tinubu

Ya ce, matsin tattalin arziƙin da rufe bodar yake jawowa ya wuce ƙima a kan ƴan kasuwa, sannan kuma ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta buɗe bodar Maje-Illo da ke Jihar Kebbi domin ƴan kasuwar su shigo da kayayyaki Najeriya.

Ya bayyana cewar, kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar ya kai na naira biliyan 177 wanda ake hada-hadar kayan abinci, dabbobi da sauran abubuwa, in da ya ce, ci gaba da rufe bodar zai kassara ƴan kasuwar ƙasashen biyu.

Da yake ƙarin haske kan labarin, wani ɗan kasuwa mai suna, Hamza Saleh Jibiya ya ce, yanzu haka akwai kwantenoni 2000 da suka maƙale a Nijar waɗanda ke ɗauke da kayayyaki masu lalacewa da marassa lalacewa.

Ya ƙara da cewar waɗanann kwatenoni na ɗauke da kayan da kuɗinsa zai kai naira biliyan 140, kuma suna can a sun maƙale a Nijar.