Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ka Gaggauta Ceton Miliyoyin Mutane Daga Matsananciyar Yunwa – Dattawan Arewa Ga Tinubu

Ƙungiyar Dattawan Arewa, NEF, ta buƙaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta yin hoɓɓasa wajen ceton miliyoyin ƴan Najeriya daga cikin matsananciyar yunwa da wahalar da suke ciki.

Dattawan Arewan dai sun bayar da wannan shawara ne a jiya Litinin ta hannun Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Ƙungiyar, Dr. Hakeem Baba Ahmed.

Dattawan sun ce, ya zama dole su yi magana, musamman a yanzu da shugaban ƙasa ke haɗa ƴan majalissarsa, ta yanda ƴan Najeriya zasu ga ci gaba a yanda ake gudanar hukunce-hukunce da tsare-tsaren gwamnatin.

Jawabin dattawan ya nuna cewar, sun amince da cewar gwamnatin ta yi kura-kurai wajen aiwatar da wasu manyan hukunce-hukunce kafin ta fahimci inda ya kamata ta sa gaba, haka kuma, ƙoƙarin gyara kura-kuran da akai ba su yi nasara ba, sai ma ƙara matsi da takura ga ƴan Najeriya.

Don haka, dattawan sun buƙaci gwamnatin Tinubu da ta gaggauta samar da sauƙin rayuwa ga miliyoyin ƴan Najeriya da ke fuskantar matsananciyar yunwa da rashin sanin makoma.

Ƙungiyar ta kuma nuna rashin gamsuwarta kan abubuwan rage raɗaɗin da aka baiwa gwamnoni, inda ta ce abin da aka ba su domin bayar da tallafi a jihohinsu zai wuya ya kawo canjin da ake buƙata a kan adadin mutanen da ke cikin matsananciyar buƙata.