Daga: Ahmed Ilallah
Tabbas, Gwamnatin Danmodi tayi gagaruman aiyuka da kawo chanje-chanje masu amfani kama da ga ilimi, lafiya, samar da aiyukan yi da sauran su, wanda suke bukatar sanarwa al’ummah da kuma wayar musu da kai.
Haka zalika, akwai yakin sunkuru da a ke yiwa wannan gwamnati, kuma da ga yayan ta, walau a Radio ko a dandalin media na zamani da makamantan su, wanda ba karamar illa take yiwa gwamnatin ba dama yi mata zagon kasa.
Batun Media, koda yake in har zaka kayi takaitaccen batu game da ‘Yan media Jigawa shine, har yanzu basu dauru a tsintsiya guda ba, kamar alamar #APC, sannan kuma babu wani tartibin tsari da layi da aka dora su, suyi ta aiki da ga wajen gwamnatin.
Kalubalen Da Ke Kan Gwamnatin Danmodi Game Da ‘Yan Media
A hakikanin gaskiya ba wai kawai jagororin siyasar Jahar Jigawa ba, mafi akasarin jagororin siyasar wannan zamani, sun gaza banabanta Dan-Duma da Dan-Kabewa. Ita fa siyasa tamkar jakar magori ce, in an zauna sai a zazzage, a ware gero da barkono da kulili, kuma a bawa kowa nasa muhimmancin.
Kafin nayi bayanin a kan wannan batu, bari in tuna mana a kwanakin nan ne fa wani mawakin siyasa, ya yi ikirarin anyi masa butulci, yana ganin wakar sa ce ta bawa APC nasara na a kalla kasha 20. Irin wannan tunani akasarin Yan Media suke tunani.
Kalubale na farko a kan jagororin siyasar wannan zamani shine, tantacewa da kuma ajiye wa duk wani dan siyasa a matsayin sa, kamar mawaki, dan sojan baka, dan media da sauran su. Duguwar mika a kan irin wannan bangarori na siyasa, kan iya damulawa Jagororin siyasa lamari.
GWAMNATIN DANMODI, a kwai abubuwa masu ban mamaki, ganin kasancewar muhimmancin yada labarai da fahimatar da al’ummah a kan aiyuka da manufofin gwamnati, amma har tsawan wannna lokaci babu wani tartibin tsari ko manhaja da a ka dora ‘Yan Media dama sauran wanda zasu iya bawa gwamnatin gudunmawa wajen fahimtar da al’ummah manufofin gwamnatin, sannan a samu bigiren tsokaci ko shawara ga gwamnatin.
GWAMANTIN DANMODI, a zahirin gaskiya, in har za a gwada gudanuwar Media Zamani ta Jahar Jigawa da sauran takwarorin ta wasu jahohin, zaka ga kan cewar da sauran rina a kaba a Jahar Jigawa.
Wani bawan Allah da muke hira da shi a kan irin wannan matsala, sai yace, ai abin mamaki a Jigawa, su Jagororin Gwamnatin a Media kamar sun fi maida hankali wajen nemawa kansu martaba a idon mutane, sun fi maida hankali wajen aiyukan Gidauniyar su ko kuma wasu aiyuka nasu na kansu a idon mutanen Jahar da kuma neman suna a wurin ‘yan mediar. Maimakon yunkurin aikin da ke gaban su, na magance matsala da aikin media ta daukakan Maigidan.
Wanda wannan karara ya sabawa aikin yiwa Maigida hidima, a siyasan ce. Amma ni ban gamsu da wannan batu ba.
Kalubalen ‘Yan Media Da Facebook Din Jigawa
Kamar yadda na fada a sama, babban kalubalen shine, sun gaza daure kansu kamar tsintsiyar #APC, akasarin su, basa tsayawa da kafar su, kusan kowa kukan wani yake tayawa, ma’ana kusan kowa dan mediar maigidan sa ne, kuma shi ya fi karewa, ba wai manufar jama’iyya ba da gwamnatin.
Har ila yau, a kwai kalubale na rashin jajircewa da fadadawa a kan ita kan ta aikin mediar da kuma fadin tunani da kara ilimi a kan harkar, ya kamata a wuce tallar hotuna kadai da banbadan ci, da kuma fada a tsakani, duka da cewa a Jama’iyya daya a ke, domin kawai banbancin fahimta, irin wannan halin yana ragewa ita kanta tafiyar mediar daraja.
Da fatan zaman farko da a kayi da maigirma gwamna zai kawo kykkywar dinke wannan kalubale domin mu kawo cigaba a wannan gwamnatin mu, mai albarka.
Ahmed Ilallah ya rubuto daga Hadejia, Jihar Jigawa.