Kamfanin Meta, mai mallakar Facebook da Instagram, ya yi barazanar dakatar da ayyukansa a Najeriya sakamakon abin da ya bayyana a matsayin “buƙatu marasa cimmuwa” daga hukumomin Najeriya da kuma tarar kusan dala miliyan 290 da ake bin shi daga wasu hukumomin gwamnati uku, kamar yadda jaridar BBC ta gano a cikin takardun kotu da ta gani jiya Juma’a.
A cewar takardun, barazanar ta Meta ta biyo bayan gazawar kalubalantar da ya shigar a kotu don hana cin tararsa, wanda kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da shi a watan Afrilu 2025, inda kotun ta dage kan dole Meta ya cika dukkan sharuɗa kafin ƙarshen watan Yuni 2025.
Hukumar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kayayyaki (FCCPC) a wata sanarwa da ta fitar a watan Yulin 2024, ta zargi Meta da karya dokokin kare bayanai da amfani da bayanan masu amfani da manhajojinsa ba tare da izini ba, tare da amfani da ƙarfin kasuwa fiye da ƙima.
WANI LABARIN: Zamu Tsare Dazukanmu, Mu Ƙarfafa Harkokin Leƙen Asiri – Tinubu
“Gaza bin sharuɗan da ake buƙata zai iya tilasta wa Meta dakatar da ayyukan Facebook da Instagram a Najeriya don kauce wa hukunci,” in ji kamfanin a cikin bayanan kotun.
Meta ya bayyana cewa sharaɗin da Hukumar Kare Bayanai ta Najeriya (NDPC) ta gindaya na neman amincewa kafin duk wani tura bayanai zuwa ƙasashen waje ba zai yiwu ba kuma ya saɓa wa dokokin Najeriya.
Hakanan, NDPC ta buƙaci Meta ya saka bidiyon gwamnati a dandalin don faɗakar da jama’a game da haɗurran amfani da bayanai, matakin da kamfanin ya ce shi ma ba zai yiwu ba.
Duk da wannan rikici, Facebook na ci gaba da zama babban dandali na sadarwa a Najeriya, musamman ga ƴan kasuwa da ƙananan kamfanoni da ke amfani da shi wajen talla da hulɗa da kwastomomi, wanda hakan ke nuna cewa dakatar da dandamalin zai kawo cikas ga tattalin arzikin dijital na ƙasa.