Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Kamfanin NNPC Ya Ƙara Farashin Man Fetur A Najeriya

Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya ƙara farashin man fetur daga ₦568 zuwa ₦855, ₦897 (dangane da wurin sayarwa), duk da ƙarancin fetur da kuma halin da ƙasar ke ciki.

Rahotanni kan sabon karin farashin sun biyo bayan furucin da NNPC ya yi na cewa masu kawo man na binsa bashin sama da dala biliyan $6.

Ƴanjaridar da suka ruwaito labarai daga Abuja da Lagos kan batun ƙarin, sun tabbatar da wannan karin farashi a yau Talata.

Rahoto daga Abuja ya nuna cewa an ƙara farashin zuwa ₦897 kan kowacce lita, yayin da wani rahoton daga Lagos ya ce gidan mai na NNPC a titin Awolowo da ke Lagos ɗin ya ƙara farashin zuwa ₦855 kan kowacce lita.

Suma sauran ƴan kasuwar man sun bi sahu wajen ƙara farashin, inda aka samu ƙarin kashi sama da 30%, inda farashin ya kai kusan ₦897 kan kowacce lita.

Rahotanni a baya sun nuna cewa an ƙara farashin man fetur a wuraren shigo da shi zuwa ₦754 kan kowacce lita.

Ana zargin cewa an sake farashin ne don ya dace da farashin man a kasuwannin duniya, da kuma rage nauyin bashi da ke kan NNPC.

Sai dai kuma, mai magana da yawun NNPC, Femi Soneye, ya musanta batun karin farashin, yana mai jaddada cewa tsohon farashin yana nan.

Tun da farko, Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata rahotannin da suka ce ta umarci NNPCL da ya sanya farashin fetur ya kai ₦1,000 a kowacce lita.