Kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya sun bayyana cewa za su iya dakatar da ayyukansu saboda bashin da ya kai naira tiriliyan 5.2 da suke bin gwamnatin tarayya.
A cewar shugabar ƙungiyar kamfanonin, Dr. Joy Ogaji, kamfanonin sun daɗe suna jure rashin biyan su kuɗin aikinsu, amma yanzu lamarin ya fi ƙarfin su.
Ta ce cikin sabon bashi akwai naira tiriliyan 1.2 daga wutar da aka samar a farkon shekarar 2025, wanda ya ƙaru da wanda ake bin gwamnati tun daga shekarar 2015.
Basussukan sun haɗa da naira tiriliyan 2 daga shekarar 2024 da kuma tiriliyan 1.9 da aka gada.
WANI LABARIN: Tsadar Taki Na Hana Noman Shinkafa Da Masara A Najeriya A Bana
“Kuɗin da ake kashewa wajen samar da wuta a kowane wata yana kai wa naira biliyan 250, amma a kasafin 2025, gwamnati ta ware naira biliyan 900 kawai,” in ji Ogaji.
Ta ce, kuma har yanzu ba a samu cikakken tabbacin samun wannan adadi ba daga gwamnati.
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya ce ana ƙoƙarin rage wasu daga cikin bashin amma bai bayyana yadda za a yi hakan ba.
Kamfanonin sun ce matsin tattalin arziƙi da rashin kuɗi na kawo barazana ga cigaban wutar lantarki a Najeriya.
Sun kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan su ko su dakatar da aiki gaba ɗaya.