Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

KATSINA: Kwastam Ta Kama Miyagun Ƙwayoyi Na Miliyoyin Nairori, Ana Zarginsu Da Ta’addanci

Hukumar Kwastam ta kama miyagun ƙwayoyi da ƙimarsu ta kai naira miliyan 692 a Katsina, abin da aka bayyana a matsayin mafi girma a tarihin rundunar a jihar.

Jami’ai sun tare motoci biyu a yankin Kongolom da wasu unguwannin kan iyaka, inda suka gano kwalaye 14 na tramadol (na kimanin naira miliyan 28), kafson fragaballin (na kimanin naira miliyan 650) da kusan kulli 200 na wiwi (kimanin naira miliyan 14) a ɓoye.

Kwamandan yankin, Abba-Aji Idriss, ya ce: “Wannan shi ne mafi girma a tarihin sashen,” yana mai ƙari da cewa “ba za a iya raba amfani da miyagun ƙwayoyi da ta’addancin da ke faruwa a wannan yanki ba; an ɓoye su a motoci kamar na yau da kullum, amma sa’a ta kasance a gare mu.”

An kama mutum ɗaya, kuma a cewar Idriss za a gurfanar da shi bayan binciken farko, tare da kira ga mazauna kan iyaka su yi aiki tare da kwastam domin daƙile safarar ƙwayoyi.

Hukumar ta bayyana cewa safarar miyagun ƙwayoyi ta fara maye gurbin shinkafa a matsayin babban haramtaccen kaya a iyakokin Arewa, abin da ke ƙara hura wutar rashin tsaro.