Ƙungiyar ƴan kishin ƙasa ta Patriots for the Advancement of Peace and Social Development (PAPSD) ta bayyana kiraye-kirayen da ake yi na kafa dokar ta-baci a Jihar Zamfara a matsayin “mugun nufi, rashin kishin ƙasa, da kuma tsarin siyasa marar adalci.”
Daraktan gudanarwa na ƙungiyar, Dr. Sani Shinkafi, ya fitar da wannan jawabi ne a jiya Asabar a Abuja, inda ya bayyana lamarin a matsayin yunƙuri na hana ci gaban da Gwamna Dauda Lawal ke ƙoƙarin samar wa a jihar.
Ya ce, “Wannan yunƙuri na neman ayyana dokar ta-ɓaci, an tsara shi ne domin tayar da zaune tsaye da tunzura al’umma, musamman domin ɓatawa gwamnatin Lawal suna, wadda ke aiki tuƙuru wajen sauya fasalin Zamfara daga jihar noma zuwa jihar masana’antu.”
WANI LABARIN: Boko Haram Sun Hallaka Sojoji A Harin Da Suka Kai Wa Rundunarsu A Yobe
Dr. Shinkafi ya soki waɗanda ke ɗaukar matasa suna turasu yin zanga-zangar kiraye-kirayen dokar ta-ɓaci, yana mai cewa “ba za a iya kwatanta halin da ake ciki a Zamfara da wanda aka samu a Jihar Ribas ba,” yana mai jaddada cewa Gwamna Lawal na aiki tare da goyon bayan mafi yawan ƴan majalisar dokokin jihar da kuma al’umma.
Ya jaddada cewa tsarin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada a sashe na 305 ne kawai ke baiwa shugaban ƙasa ikon ayyana dokar ta-ɓaci, kuma babu wani lokaci a yanzu da ke nuna cewar jihar Zamfara na buƙatar hakan.
“Yanzu haka, idan aka kwatanta da shekarun baya, an samu ci gaba wajen inganta tsaro a jihar, kuma mafi yawan hotuna da bidiyoyin da ke yawo a kafafen sada zumunta na harin baya ne da ake sake yaɗawa don tayar da hankali,” in ji shi.
Dr. Shinkafi ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da manyan hafsoshin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don daƙile hare-haren da ke faruwa, tare da buƙatar Gwamna Lawal da ya kira babban taron tsaro na gaggawa da ya haɗa da shugabannin addini, na gargajiya, ƙananan hukumomi da ƙungiyoyin farar hula don samar da hanyar warware matsalar tsaro a jihar.