Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Kotu Ta Ce A Ci Gaba Da Tsare Wanda Ake Zargi Da Satar Ganda A Kano

An gurfanar da wani matashi ɗan shekara 23 mai suna Abdulwahab Yusuf  a wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano bisa zarginsa da satar fatar shanu wadda aka fi sani da ganda, wadda kuɗinta ya kai naira 8,500.

Ana tuhumar Abdulwahab, wanda ɗan Unguwar Tukuntawa da ke Birnin Kano ne da laifin yin sata.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa, Alƙali Lawal Abubakar ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 22 ga watan Agusta domin bayar da ƙwarya-ƙwaryan hukunci.

Tun da farko dai, ɗansanda mai shigar da ƙara, Sufeta Abdullahi Wada, ya faɗa wa kotun cewa, wanda aka yi wa satar mai suna Fatihu Auwal, wanda shi ma mazaunin Unguwar Tukuntawa ne, ya sanar da cewar an yi masa satar ga jami’an ƴansanda na Ofishin Ƴansanda na Fagge a ranar 5 ga watan Agusta.

Sufeta Abdullahi Wada ya ce, wanda ake zargin ya shiga rumfar wanda aka yi wa satar ne inda ya sace masa ganda.

(NAN)