Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Kotu Ta Tura Shahararren Ɗan TikTok Gidan Yari Bisa Yaɗa Ƙaryar Tinubu Ya Mutu

Wata kotun majistare a Abuja ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wani mai amfani da kafar TikTok, Ghali Isma’il, a gidan gyaran hali na Keffi bisa zargin yada ƙaryar cewa Shugaba Bola Tinubu ya mutu.

An gurfanar da shi ne bayan jami’an DSS sun kama shi, inda aka tuhume shi da laifin yaɗa labarin ƙarya da cutar da munanawa gwamnati, bisa dokokin Penal Code.

A cikin laifi na farko da aka karanta masa, an bayyana cewa ya yi zargin cewa Shugaban ya kamu da wata cuta sakamakon dafa masa abinci mai guba, yana mai cewa ya tabbatar da hakan daga “majiyoyin hukuma.”

WANI LABARIN: Rikicin SDP Ya Ƙara Ta’azzara: NEC Ta Rushe Shugabancin Jam’iyya, Ta Ce Ba Ta San El-Rufa’i A Cikinta Ba

A laifi na biyu, an ce ya yunƙurin ta da jijiyoyin wuya da kawo ƙasƙanci ga gwamnatin da ya bayyana ta hanyar wallafa labarin da ba shi da tushe a TikTok.

Alƙali Ekpeyong Inyang ya ƙi bayar da belinsa, yana mai dagewa cewa, Isma’il ya ci gaba da zama a tsare har zuwa 19 ga watan Agusta.

Wannan shari’ar na zuwa ne bayan wani malami a Amurka, Farooq Kperogi, ya nemi afuwa kan wani labari da ya fitar cewa Buhari da matarsa sun rabu kafin rasuwarsa.

Haka kuma, an ambato cewa Simon Ekpa da Nnamdi Kanu na fuskantar shari’a bisa zargin amfani da kafafen sada zumunta wajen tayar da tarzoma da cin fuska ga gwamnati, inda su kuma suka ce saƙonnin da suka fitar “ba su da wata manufa fiye da barkwanci ko ƙirƙirar abun nishaɗi.”