Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa hana mata masu hidimar ƙasa (NYSC) sanya siket saboda wasu dalilai ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
A hukuncin da mai shari’a Hauwa Yilwa ta yanke a ranar 13 ga Yuni 2025, kotun ta bayyana cewa tilasta wa mata sanya wando kawai na hana ƴancin su na addini da mutuncin ɗan Adam kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Shari’ar ta samo asali ne daga ƙorafe-ƙorafe na Miss Ogunjobi Blessing da Miss Ayuba Vivian, waɗanda suka yi iƙirarin cewa sanya wando ya saɓawa imaninsu na Kiristanci da kuma ayar Deuteronomiyom 22:5.
WANI LABARIN: Gwamnonin Da Ke Son Shiga Haɗakar ADC Na Tsoron Ƙuntatawa Daga Gwamnatin Tinubu
Kotun ta ce “ƙin amincewa da siket ga mata masu ƙin wando saboda addini ya saɓa wa kundin tsarin mulki,” tare da ba da umarnin cewa NYSC ta amince da wannan canji da kuma karrama ƴan hidimar da abin ya shafa.
Alƙaliyar ta kuma ce wulaƙanci da suka fuskanta daga jami’an NYSC ya zama take haƙƙinsu na addini da martaba.
Duk da masu ƙorafin sun nemi diyya ta naira miliyan 10 kowannensu, kotun ta umarci a ba su naira dubu 500 kowanne a matsayin diyya.
Hukuncin ya umarci Hukumar NYSC da ta amince da siket ga duk wata mace da ke da dalilan addini da kuma bayar da takardun kammala hidima ga waɗanda aka hana kan wannan dalilin.