Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Kotu Ta Yankewa G-Fresh Hukuncin Ɗauri Bisa Cin Zarafin Naira

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke wa wani shahararren mai amfani da TikTok, Abubakar Ibrahim, wanda aka fi sani da G-Fresh, hukuncin ɗauri na wata biyar bisa laifin cin mutuncin kuɗin Najeriya.

Mai shari’a Sale Musa Shuaibu ne ya yanke hukuncin bayan hukumar EFCC ta gurfanar da G-Fresh a gaban kotu bisa zargin watsa Naira a bainar jama’a.

G-Fresh ya amsa laifukan da ake tuhumarsa da su, inda kotun ta ba shi zaɓin biyan tara na Naira dubu ɗari biyu ko kuma a ɗaure shi.

WANI LABARIN: Gwamnatin Tinubu Ta Mayarwa Da Kwankwaso Martani Kan Zargin Nuna Wariya Ga Arewa

An same shi da laifin watsa takardun Naira dubu-dubu a wajen bikin buɗe wani shago da Rahama Sa’idu, wata sananniyar ƴar TikToka, wadda aka yi a unguwar Tarauni a bara.

G-Fresh wanda ke da mabiya fiye da miliyan ɗaya da rabi a TikTok, ya shahara ne ta hanyar barkwanci da waƙa da nufin nishaɗantarwa da nuna iyawa.

Rahotanni sun ce G-Fresh ya taɓa shiga hannun hukumar Hisbah a Kano bisa zargin faɗin kalmomi da suka saɓa wa tarbiyya.

A cewar wani jami’in Hisbah, Aliyu Usman, an kama shi ne bayan da ya yi kuskuren karanta Suratul Fatiha a lokacin bikin Sallah na ranar 11 ga Afrilu, abin da ya janyo suka daga al’umma.