Kutun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa a yau Laraba ta yanke hukuncin cewar, waɗanda su ke ƙalubalantar zaɓen shugaban ƙasa, sun gaza gabatar da hujjojin da ke nuni da cewar akwai kuskure a bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya ci zaɓen ranar 25 ga watan Fabarairu, 2023.
Ɗan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da na jam’iyyar LP, Peter Obi da kuma jam’iyyar APM sun ƙalubalanci nasarar Bola Ahmed Tinubu a kotun bisa zarge-zargen da su ka shafi zargin maguɗin zaɓe da rashin cancantar tsayawa takara ga Bola Ahmed Tinubu.
Kotun mai alƙalai biyar, ƙarƙashin jagorancin Babban Alƙali Haruna Tsammani sun karanta ƙorafe-ƙorafe da kuma hukuncin da aka yanke a wani dogon zama da aka gabatar yau a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya da ke Birnin Tarayya Abuja.
Mafi yawan hukunce-hukuncen da kotun ta yi a kan ƙararrakin sun kasance na watsi da ƙara saboda gazawar ma su ƙorafi wajen kare iƙirarinsu da zarge-zargensu a kan waɗanda su ke ƙara.
Alƙalan sun yi watsi da iƙirarin Peter Obi na jam’iyyar LP da su ka haɗa da zargin aikata ba daidai ba a ɓangaren Tinubu, rashin cancantar tsayawa takararsa da kuma rashin ingancin zaɓen da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta yi wanda ya bai wa Tinubun nasara.
KARANTA WANNAN: A Ƙarshe Dai NNPP Ta Kori Kwankwaso Saboda Yi Wa Jam’iyyar Zagon Ƙasa
Haka kuma kotun ta yi watsi da zarge-zargen da Atiku Abubakar ya yi na cewar an tafka maguɗi, sannan kuma Tinubu bai cancanci tsayawa takara ba saboda takardun bogi da ya gabatar da kuma batun kasancewar Tinubu mai ɗauke da shaidar kasancewa ɗan ƙasar Guinee da sauran ƙorafe-ƙorafe da dama.
A ɓangaren jam’iyyar APM kuma da ke ƙalubalantar zaɓen kan cancantar Kashim Shettima na yi wa Tinubu takarar mataimaki, kotun ta bayyana cewar jam’iyyar ta gaza gabatar da hujjojin da su ke tabbatar da iƙirarinta.
Tun dawowar mulkin demokaraɗiyya a Najeriya a shekarar 1999 dai, ba a samu wata ƙarar ƙalubalantar cin zaɓen shugaban ƙasa da tai nasara ba.
A yanzu dai ma su ƙorafin, Atiku, Obi da APM na da damar ɗaukaka ƙara cikin kwanaki 60 daga ranar wannan hukunci zuwa Kotun Ƙoli domin ta yi watsi da hukuncin Kotun Ƙararrakin Zaɓen.
A watan Yunin da ya gabata ne, ma su sanya ido kan yanda ake gudanar da zaɓuka na Tarayyar Turai su ka bayyana cewar an samu matsaloli a zaɓen da aka gudanar a watan Fabarairun da su ka haɗa da na gazawar na’urorin zaɓe da kuma rashin gaskiya, abin da ya sa al’umma su ka rage sa ransu a kan tsarin zaɓen ƙasar.
A ƙasar da ke da mutane sama da miliyan 200, wanda a cikinsu mutane miliyan 87 ke da katin zaɓe, Tinubu ya samu nasarar ne da ƙuri’u miliyan 8.79, mafi ƙaranci kenan da wani shugaban ƙasa ya samu tun bayan dawowar ƙasar kan mulkin demokaraɗiyya.