Kotun Ƙoli ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekaru biyar kan tsohon Ɗan Majalissar Wakilai, Farouk Lawan bisa kama shi da laifin karɓar cin hanci na dala 500,000 daga sanannen ɗan kasuwar nan Femi Otedola.
An dai binciki Farouk Lawan ne kan zargin karɓar cin hancin a lokacin binciken majalissa kan tallafin mai a shekarar 2012.
A hukuncin ƙarshe na Kotun Ƙolin da Alƙali John Okoro ya jagoranta, Alƙali Tijjani Abubakar ya bayyana cewar, Kotun Ƙolin ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da Farouk Lawan yai saboda rashin hujjoji.
A ɗaukaka ƙarar da Farouk Lawan yai a ranar 24 ga watan Fabarairu, 2022 ya buƙaci Kotun Ƙolin tai watsi da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da yanke wa masa hukuncin zaman fursuna na shekaru biyar.
A wancan hukunci na Kotun Ɗaukaka Ƙarar, kotun ta ragewa Farouk Lawan adadin shekarun da zai yi a gidan yari daga bakwai zuwa biyar.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ce ta yanke masa hukunci a ranar 22 ga watan Yuni, 2021 bisa kama shi da laifukan da suka haɗa da neman cinhanci, yarda da karɓar cinhanci da kuma karɓar cinhanci dala 500,000 daga sanannen ɗankasuwa Femi Otedola.