Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta sallami tare da wanke tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido da sauransu kan zargin cin hanci.
Kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Alƙali Adamu Waziri a yau Talata ta bayyana cewa, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ba ta hurumin ta saurari ƙarar kamar yanda ta saurara a baya.
A baya dai, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ƙi karɓar ƙorafin wanda ake ƙara na cewar babu hujjar tuhumarsa da ake kan zargin cin hanci da rashawa.
Daga nan ne, Sule Lamido ya ɗaukaka ƙara a gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara yana ƙalubalantar hukuncin ƙaramar kotun.
A Karanta Wannan: CIRE TALLAFI: Gidajen Mai Sun Fara Shirin Korar Ma’aikata
An dai kama Sule Lamido ne a watan Satumba, 2016 a gaban Alƙali Adeniyi Ademola kan zargin laifuka guda 43 da suka shafi haɗa baki, wasa da ofishi da kuma almundahana da kuɗaɗe da yawansu ya kai naira biliyan 1.351.
An zarge shi ne tare da ƴaƴansa guda biyu, Aminu da Mustapha, tsohon mai temaka masa, Wada Abubakar da kuma kamfanoni guda huɗu, Baimana Holdings Ltd, Bamaina Company Nigeria Ltd, Bamaina Aluminium Ltd, Speeds International Ltd da kuma Batholomew Darlington Agoha.
Shari’ar da aka ɗebe shekaru kusan bakwai ana yi, ta samu tsaiko ne bayan ritayar da Alƙali Adeniyi Ademola ya yi.
Daga baya an miƙa shari’ar ga Alƙali Chukwu, wanda ya rasu, abin da ya sa dole aka miƙa ta ga Alƙali Babatunde Qaudri.
Bayan an yiwa Alƙali Quadri canjin gurin aiki, sai aka miƙa shari’ar ga Alƙali Ijeoma Ojukwu, wanda daga nan ne aka fara sabuwar shari’ar duk da kafin haka EFCC ta gabatar da shaidarta ta ƙarshe.
