
An samu ƙarin farashin ɗakunan otal-otal da ke Makkah a watan Ramadan na bana.
Shi ne farashi mafi tsada cikin shekara uku, inda ya kai kashi 80 cikin 100 kamar yadda yake a ƙididdigar da hukumar kula da aikin hajj da umrah ta Makkah ta fitar.
Farashin otal ɗin a azumin bana ya ƙaru saboda yawan buƙata musamman a cikin kwana 10 na ƙarshen watan.
Wani nazari da Al-Eqtisadiah business daily ta yi game da karɓar otal a tsakiyar birnin Makkah cikin goman ƙarshe na Ramadana, farashin ya kai tsakanin SR3,000 zuwa SR9,000 a kullum, idan dakin otal ɗin za a yi amfani da shi ne a cikin goman ƙarshe.
Shugaban hukumar, Abdullah Al-Qadi ya ce farashin ɗakunan otal ɗin ya ta’allaƙa ne a kan wasu batutuwa, da kuma ƙarin buƙata da kasancewar kusancin wajen da masallacin Harami.
Ya ce abin da ya bambanta farashin ɗakunan otal ɗin a Makkah shi ne kasancewar ɗakunan suna tsakiyar birnin Makkah inda farashinsu kan tashi idan azumi ya gabato, sannan kuma su ninka a goman ƙarshe na watan.