Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Kusan Dukkan Ɗaliban Da Suka Rubuta JAMB Ta Bana Sun Gaza Samun Rabin Makin Jarabawar

Fiye da ɗalibai miliyan ɗaya da rabi daga cikin ɗalibai 1,955,069 da suka zauna jarrabawar Unified Tertiary Matriculation Examination (UTME) ta shekarar 2025 sun kasa samun maki 200, in ji hukumar JAMB a wani rahoto na ƙididdiga da ta fitar a yau Litinin.

JAMB ta bayyana cewa ɗalibai 420,415 ne kaɗai suka samu maki fiye da 200 a jarabawar bana, inda kimanin kaso 75% na waɗanda suka zauna jarrabawar suka kasa cin 200.

Hakanan, kaso ƙasa da 1% ne kawai suka samu maki fiye da 300, yayin da wasu ɗaliban da aka amince su zauna jarrabawar duk da cewa ba su kai shekaru ba suka kai kashi 1.16% da suka yi fice.

WANI LABARIN: Masu Farauta 13 Sun Ɓace, Bayan Faɗawa Maɓoyar Lakurawa A Sokoto

“Ɗalibai 40,247 da shekarunsu basu kai na doka ba sun zauna jarabawar saboda bajintar da suka nuna, amma ɗalibai 467 ne kaɗai daga cikinsu suka cimma makin da aka gindaya musu,” in ji sanarwar.

Hukumar ta ƙara da cewa ana bincike kan wasu 2,157 da ake zargi da hannu a wajen jarrabawar da kuma wasu 97 da aka tabbatar da karya doka.

Bugu da ƙari, an bayyana cewa ɗalibai 71,701 ba su samu halartar jarrabawar ba, yayin da wasu ke fuskantar matsalar hotunan yatsu biometrics da ake ƙoƙarin warwarewa kafin a sake musu jarrabawar.

JAMB ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a saki sakamakon ɗalibai makafi da kuma waɗanda ke ƙarƙashin rukunin JEOG.