Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Babban Lauyan Najeriya, Farfesa Tahir Mamman a matsayin sabon Ministan Ilimi na Najeriya.
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Kafafen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Ajuri Ngelale ne ya bayyana naɗin jiya Laraba a Abuja.
Sanarwar ta kuma bayyana Yusuf Tanko Sununu a matsayin wanda zai kasance Ƙaramin Ministan Ilimin.
Farfesa Mamman wanda tsoho Babban Darakta Janar ne na Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Najeriya a tsakanin shekarun 2005 da 2013, ya zama Ministan Ilimin ne bayan Alhaji Adamu Adamu ya kammala tare da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Farfesan zai kasance Ministan Ilimi na 47 kenan tun lokacin da Najeriya ta fara yin Ministan Ilimi da kanta a shekarar 1958.
Wane Ne Farfesa Mamman
An haifi Tahir Mamman a shekarar 1954, a garin Michika da ke Jihar Adamawa.
Ƙwararren masanin shari’a ne, wanda ya samu digirinsa na farko, LLB, daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 1983, sannan shekara guda bayan nan ya kammala makarantar horon aikin lauya, inda ya zama cikakken lauya.
Ya samu aiki da Jami’ar Maiduguri, UNIMAID a matsayin malamin ɓangaren koyon shari’a, inda daga baya ya zama shugaban tsangayar koyon ilimin shari’a ta jami’ar.
Farfesa Mamman ya samu yin karatun digirinsa na biyu a Jami’ar Warwick ta Birnatiya, lokacin kaɗan bayan nan ya samu shaidar digirin digirgir Ph.D.
Ya zama Darakta Janar na Makarantar Horon Aikin Lauya ta Najeriya a shekarar 2005, inda ya samar da ci gaban da ake buƙata cikin shekaru 8 da yai a makarantar.
Kafin wannan muƙamin, Farfesa Mamman, ya riƙe Mataimakin Darakta na reshen Kano na Makarantar Horon Aikin Lauyan.
Mamba ne shi a Ƙungiyar Ƙasa da Ƙasa ta Makarantun Koyon Aikin Lauya da ke da cibiya a birnin Washington na Amurka.
A shekarar 2015 ne aka tabbatar da Farfesa Mamman a matsayin Babban Lauyan Najeriya wato SAN saboda irin gudunmawar da ya bayar a ɓangaren bunƙasa ilimin lauya a Najeriya.
A daidai wanna lokaci da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Mamman Ministan Ilimi, shi ne Shugaban Jami’ar Baze, jami’a mai zaman kanta da ke tsakiyar Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Farfesan ya kuma samu lambar girmamawa ta ƙasa ta Officer of the Order of the Niger (OON), saboda irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban Najeriya.
A yanzu dai za a jira a ga irin ƙoƙarin da Farfesa Tahir Mamman zai yi wajen kawo ƙarshen tulin matsalolin da suka addabi harkar neman ilimi a Najeriya.