Daga: Lukman Dahiru
An samu ɓarkewar cutar amai da gudawa a Ƙaramar Hukumar Kirikasamma ta Jihar Jigawa, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai, yayin da aka kwantar da wasu da dama a asibiti.
Shugaban kula da lafiyar al’umma na yankin, Musa Abdullahi Diladige ne, ya tabbatar da barkewar cutar a yankunan Malori, Maikintari, Dilmari, Kirikasamma, da wani ɓangare na ƙauyen Baturiya.
Diladige, ya bayyana cewa wadanda abin ya shafa na fama da alamomin rashin lafiya masu tsanani kamar gudawa, kumburin ciki, amai, da kuma zazzabi.
Ya kuma ce, an tura ma’aikatan lafiya zuwa yankunan don samar da agajin gaggawa, haka kuma hukumomi sun ɗauki matakin gaggawa ta hanyar sayan magungunan da ake buƙata don fara jinyar masu cutar.
Daraktan gudanarwa da ayyukan gama-gari, Idris Gambo Abubakar, ya yi alƙawarin bayar da goyon bayan da ake buƙata don daƙile yaɗuwar cutar.
Ana kyautata zaton ruwan sama mai tsanani da aka samu a yankin ne ya haifar da ɓarkewar cutar, inda gine-gine suka lalace kuma hanyoyin samar da ruwan sha suka gurɓace.