Saboda yajin aikin gargaɗin da NLC ta sanar da farawa a yau, kwamitin wucin gadi da ke bincikar badaƙalar ɗaukar ma’aikata a ma’aikatu da hukumomi, a jiya Litinin ya sanar da ɗage ci gaba da aikinsa har sai ranar Alhamis 7 ga watan Satumba.
Kwamitin dai na aikin bincikar zarge-zargen badaƙalar da ake tafkawa wajen ɗaukar ma’aikata da kuma rashin aiwatar da manhajar IPPIS yanda ya kamata.
Shugaban Kwamitin, Hon. Yusuf Adamu Gagdi, ya bayyana cewar an ɗage ci gaba da zaman sauraron ƙorafe-ƙorafe a kwamitin domin bayar da dama ga ma’aikatu don su gabatar da bayanansu.
Da yake magana kan halin karɓar kuɗaɗe domin ɗaukar ma’aikata da wasu jami’an gwamnati ke yi, Gagdi ya tabbatarwa da ƴan Najeriya cewar Majalissar Tarayya ta 10 za ta magance matsalar.
Gagdi ya ce, kwamitinsa zai gabatar da shawarwari a rahotonsa tare da yin alƙawarin cewar afuwar da aka bai wa ma’aikatu na rashin tallata gurbin aiki za ta zo ƙarshe.