Sama da ma’aikata 700 ne na Hukumar Kula da Ilimin Arabiya da Addinin Musulunci, NBAIS, suka koka kan rashin biyansu alabashin watanni 17 da suke bin gwamnati.
Ma’aikatan sun kuma bayyana cewa, sun cika dukkan wasu ƙa’idoji na yin rijista da tsarin biyan albashi na IPPIS don biyansu albashin, amma har yanzu ba su ji komai ba.
Masu zanga-zangar, a wata sanarwa da suka fitar mai taken ‘Ƙorafi kan Rashin Biyan Albashi’, wadda ta samu sa hannun, Shugabansu, Muhammad Suleiman; Sakatarensu Benjamin Ishiaka da kuma Jami’in Hulɗa da Jama’a, Abdulsalam Ibrahim a jiya Asabar, sun bayyana cewa, wasu daga cikinsu an ware su an biya su, yayin da aka ƙyale saura.
KARANTA WANNAN: WAEC Ta Saki Sakamakon Jarabawar 2023, Ta Riƙe Sakamakon Ɗalibai 262,803
Sanarwar ta bayyana cewar, ma’aikatan sun samu aiki da NBAIS ne a watan Janairu na shekarar 2021 sannan kuma sun yi rijista da IPPIS a watan Disamba na shekarar, amma har kawo yanzu waɗanda ba su fi kaso 30 cikin 100 nasu ba ne suka sami albashi, yayin da aka bar kaso 70 cikin 100 babu komai tsawon watanni 17.
Ma’aikatan sun bayyana wannan yanayi da suke ciki a matsayin wanda ya jefa su cikin mawuyacin hali su da iyalansu, bayan sun bar aiyukan da suke yi a baya da kwaɗayin samun mafificiyar rayuwa ta hanyar karɓar aikin na NBAIS.
Lokacin da aka tuntuɓi Jami’in Yaɗa Labarai na Hukumar NBAIS, Muhammad Sambo, ya tabbatar lamarin, inda ya ce, hukumar ba ta da ikon riƙewa wani ma’aikaci albashi idan har gwamnati ta yi niyyar biyansa.
Masu zanga-zangar dai sun yi kira ga gwamnati da ta saurari kokensu, tare da warware musu matsalolin da suke ciki su da iyalansu.