Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Majalisar Dattawa Ta Yi Gargaɗi Kan Kwararowar Ƴan Ta’adda Daga Ƙasashen Ƙetare Zuwa Arewacin Najeriya

Majalisar Dattawa ta bayyana damuwa kan kwararowar ƴan ta’adda na ƙasa da ƙasa daga Mali da Burkina Faso, da ke aiki a ƙarƙashin ƙungiyar Lakurawa, zuwa jihohin Kebbi, Sokoto, da Kaduna a yankin arewa maso yamma, da kuma Jihar Neja a arewa ta tsakiya. 

Bayanan da aka gabatar yayin zaman majalisar dattawan sun nuna cewa lamarin na ƙara dagula matsalar tsaro a ƙasar. 

Wannan ya zo ne bayan irin wannan gargaɗin daga Majalisar Wakilai, Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), da wasu fitattun shugabannin arewa, ciki har da sarakunan gargajiya, da suka yi ƙorafi kan taɓarɓarewar tsaro a yankin. 

Majalisar ta yi kira ga sojojin Najeriya da su samar da hanyoyin gargaɗi tun da wuri, tare da ƙarfafa matakan tsaro a al’ummomin da abin ya shafa, don hana yaɗuwar ayyukan ƙungiyar ta’addan. 

Ƴan majalisar sun kuma yi kira ga samun haɗin gwiwa tsakanin sojoji, al’ummomi, da sauran hukumomin tsaro.

Sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta tura tawagar tantance ɓarnar da ƴan ta’addan suka yi tare da gano buƙatun gaggawa na taimakon iyalan da abin ya shafa. 

Ƴan majalisar sun yi shiru na minti ɗaya domin girmama waɗanda aka kashe a hare-haren baya-bayan nan, musamman a Jihar Kebbi, inda aka kashe mutane 17 tare da ƙona gidaje a wani mummunan hari da aka kai makonni biyu da suka wuce. 

Sanata Yahaya Abdullahi (PDP, Kebbi ta Arewa), wanda ya ɗauki nauyin ƙudirin da aka yi wa take da “Buƙatar Gaggawa Ga Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakai Masu Tsauri Kan Ƴan Ta’addan Lakurawa”, ya bayyana cewa ƙungiyar ta shigo Najeriya ta ƙananan hukumomin Illela, Tangaza, da Silame na Jihar Sokoto. 

Daga nan ne ƴan ta’addan suka kai hare-hare kan ƙananan hukumomin Augie da Arewa na Jihar Kebbi, inda aka kashe sama da mutane 20 tare da sace dabbobin da darajarsu ta kai miliyoyin nairori. 

Abdullahi ya yaba wa sojoji bisa gaggawar korar ƴan ta’addan tare da dawo da dabbobin da aka sace. 

Sai dai ya ja kunnen cewa girman tasirin ƙungiyar na ƙara zama barazana, inda ya yi gargaɗin cewa rashin ɗaukar matakai masu tsauri na iya basu damar samun ƙafa a arewacin Najeriya baki ɗaya. 

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin ya bayyana wannan lamarin a matsayin babbar matsalar tsaro ta ƙasa da ƙasa, yana mai cewa: “Waɗannan ƴan kasar waje sun mamaye ƙasar, dole mu ɗauki matakin gaggawa don dakatar da su.”

Sanata Aminu Tambuwal (PDP, Sokoto ta Kudu) ya tuna irin waɗannan hare-hare a shekarar 2018 a lokacin da yake gwamna a Jihar Sokoto, inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki wannan barazanar da muhimmanci matuƙa. 

Sanata Adamu Aliero (PDP, Kebbi ta Tsakiya) ya jaddada buƙatar sake nazarin ƙudurorin da majalisar dattawa ta gabatar a baya kan ta’addanci, yana mai nuna damuwar cewa ba a aiwatar da shawarar da aka bayar a baya yadda ya kamata ba. 

“Mun tattauna sosai a majalisun dattawa na takwas da tara kan yanda za a daƙile ta’addanci da ƴan bindiga. Yanzu lokaci ne na tabbatar da aiwatar da waɗancan ƙudurorin,” in ji shi. 

Kiran da majalisar dattawan ta yi na ɗaukar mataki ya nuna gaggawar magance ƙaruwar matsalar tsaro, wacce ke barazana ba kawai ga jihohin da abin ya shafa ba, har ma da zaman lafiyar ƙasa baki ɗaya.