Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Malam Adamu Foundation Zata Ɗau Nauyin Karatun Ɗaliban Jigawa A Khadija University Majia

Gidauniyar Malam Adamu Foundation (MAF) ta Alhaji Musa Adamu Majia mamallakin Jami’ar Khadija da ke Majia a Jihar Jigawa zata ɗau nauyin karatun ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi a Khadija University Majia.

MAF ta tanadi ɗaukar nauyin karatun ne domin samar da cikakkiyar dama ga ɗaliban ta samu karatun jami’a kyauta.

Gidauniyar ce zata biya kuɗin rijista ga dukkan ɗaliban da suka samu nasarar shiga shirin domin samun karatun digiri a fannoni daban-daban na Khadija University, Majia.

Masu morar wannan tallafi zasu samu damar karantar ɗaya daga cikin darussa masu zuwa gwargwadon jarabawar JAMB da SSCE da suke da ita:

  1. Bsc. Economics
  2. BSc. Entrepreneurship
  3. BSc. Accounting
  4. BSc. Mass Communication
  5. BSc. Criminology and Security Studies
  6. BSc. Software Engineering
  7. BSc. Cyber Security
  8. BSc. Computer Science
  9. BSc. Physics and Electronics
  10. BSc. Biology
  11. BSc. Chemistry
  12. BSc. Mathematics
  13. Nursing
  14. Medical Lab
  15. Physiotherapy

Ƙa’idojin da ake so wanda zai nemi morar wannan tallafin karatun ya cika sun haɗa da kasancewa ɗa ko ƴar asalin Jihar Jigawa.

Haka kuma dole ne mai neman ya kasance ya ci jarabawar JAMB ta shekarar 2022 ko 2023 da maki aƙalla 130.

Haka kuma dole ne mai neman ya kasance yana da CREDITS 5 a jarabawarsa ta kammala sakandire waɗanda dole ya kasance akwai darasin Turanci da Lissafi a ciki.

Ƴan Jihar Jigawan da suka cancanci neman wannan tallafin karatu, zasu ziyarci ɗaya daga cikin jerin waɗannan makarantu masu zuwa:

  1. Government Day Senior Secondary School Gagarawa
  2. Government Unity Secondary School Maigatari
  3. Government Girls Secondary School Sule Tankarkar
  4. Government Science Secondary School Lautai
  5. Government Girls Unity Secondary School Malam Madori
  6. Government Unity Secondary School Fantai
  7. Science Secondary School Kafin Hausa
  8. Government Day Senior Secondary School Kiri Kasamma
  9. Government Girls Arabic Secondary School Birniwa
  10. Government Day Secondary School Auyo
  11. Government Girls Secondary School Guri
  12. Government Girls Secondary School Kaugama
  13. Roni Computer Government Girl Secondary
  14. Government Girls Unity Kazaure
  15. Government Technical Karkarna
  16. Government Day Secondary School Gwiwa
  17. Government Unity Secondary School Ringim
  18. Government Girls Science Secondary School Taura
  19. Government Girls Secondary School Garki
  20. Government Technical College Babura
  21. Government Girls Secondary School Jahun
  22. Government Junior Secondary School Miga
  23. Government Unity College Birnin Kudu
  24. Federal Government College Kiyawa
  25. Government Junior Secondary School Yayari
  26. Government Girls Unity College Gwaram
  27. Government Unity Commercial Secondary School Dutse

Duk mai buƙatar morar wannan tallafi zai sayi takardar cike bayanansa kan naira 5,000 kacal a waɗannan santoci, sannan za a rufe sayar da takardun a ranar Juma’a 2 ga watan Fabarairu, 2024.

Domin neman ƙarin bayani za a iya tuntuɓar waɗannan lambobi: 08038751126 ko 07069671389.

Ko kuma a ziyarci shafin yanar gizo na Malam Adamu Foundation a wannan adireshin: www.mafscholarship.com.ng