Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Malamar Makaranta Ƴar Shekara 74 Na Fuskantar Ɗaurin Shekara 600 Saboda Lalata Da Saurayi

Wata tsohuwar malamar makaranta ƴar shekara 74 a duniya mai suna, Anne N. Nelson-Koch na fuskantar ɗaurin shekaru 600 a gidan yari bayan an kama ta da laifin yin lalata da saurayin yaro a wata makarantar kuɗi da ke Wisconsin.

Jaridar DAILY MAIL ta rawaito cewa, kotun Monroe County ta kama Nelson-Koch da laifin aikata laifuka 25 da suke da alaƙa da cin zarafin saurayin a lokuta da dama tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017.

Rahoton ya nuna cewa, malamar na ɗaukar yaron zuwa wani gidan ƙasa a makarantar tana lalata da shi, wanda a lokacin tana da shekaru 67 a duniya shi kuma yana ɗan shekara 14.

Masu shigar da ƙara sun buƙaci da a ci gaba da tsare Nelson-Koch har zuwa lokacin da za a gama yanke hukunci a ranar 27 ga watan Oktoba, sai dai kuma alƙalin kotun, Alƙali Richard Radcliffe ya bayar da belinta bayan an maƙala mata na’urar sanin inda mutum yake.

Mataimakin Mai Shigar da Ƙara da Gunduma, Sarah Skiles wadda ta shigar da ƙarar ta ce, yaron da aka ci zarafin mai matuƙar ƙoƙari ne a makaranta.