Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Manyan Ƴan Kasuwa Sun Yi Tir Da Rahoton NBS Kan Cigaban Tattalin Arziƙin Najeriya

Rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Kasa (NBS) wanda ya nuna ƙaruwar tattalin arziƙi da kashi 3.46% da kuma raguwar rashin aikin yi zuwa kashi 4.6% ya gamu da suka daga kungiyar ƴan kasuwa ta NACCIMA. 

Shugaban NACCIMA, Dele Kelvin Oye, ya bayyana cewa alƙaluman ba su dace da halin da ƴan Najeriya ke ciki ba. 

“Wannan bayanan ba su ɗauki ƙaruwar haraji, hauhawar farashi, da matsalolin dokoki da ke takura kasuwanci da janyo jari daga waje ba,” in ji Oye. 

Ya buƙaci a gudanar da sauye-sauye don rage ciwo bashi, inganta haɗin kai da kamfanoni masu zaman kansu, da kuma magance rashin aikin yi, wanda ba a cika bayyana gaskiyar sa ba saboda yawaitar marasa aikin. 

“Waɗannan alƙaluman suna nuna hoton da ba na gaskiya ba. Ainihin cigaban tattalin arziƙi dole ne ya haifar da ingantacciyar rayuwa ga al’umma,” Oye ya faɗa a ƙarshe.