Tsohowar wadda aka miƙa sunanta domin kasancewa minista a gwamnatin Tinubu, Maryam Shettima wadda aka fi sani da Maryam Shetty, ta bayyana janye sunanta daga jerin ministoci a matsayin ƙaddarawar Ubangiji.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu dai ya janye sunan Maryam Shetty daga cikin ministocinsa kwana biyu bayan ya miƙa shi Majalissar Dattawa, tare da maye gurbinta da wata ƴar Jihar Kano, ƴar siyasar gidan Ganduje a jiya Juma’a.
A wata sanarwa da ta saki yau Asabar, Shetty ta ce, ba zata bari abin da ya faru ya sare mata gwuiwa daga yarda da Najeriya ba.
Ta kuma nuna godiyarta ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da kuma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.
Maryam Shetty ta ce, “Na tsinci kaina a tsakiyar muhimmin yanayin siyasa na Najeriya. Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a wani yunƙuri da ya jawo min gagarumar daraja, ya zaɓe ni a matsayin wadda yake so ya naɗa minista. A matsayi na na wadda ta fito daga cikin ƴan gargajiya a Arewacin Najeriya wannan na nufin wani muhimmin sauyi na shigar da kowa domin a dama da shi.

“Farinciki da alfaharin da na ji kan tura suna na abu ne da ya fi ƙarfin a furta. Hakan na nuni da ƙwarewa ta, hangen nesa na, da kuma alamar cewa, ƙasarmu ta shirya tunkarar goben da zata baiwa matasan mata kamar ni, har ma daga cikin ƴan gargajiya a Najeriya damar riƙe muƙamin da zai zama mai tasiri da ƙarfi (wajen tafiyar da al’amura.)
“Duk da dai yanayin rayuwa na rashin tabbas, ya jawo an janye miƙa sunana da aka yi. A wajen wasu, wannan zai zama kamar koma-baya ne, amma a imanina na a matsayi na na cikakkiyar Musulma hakan ya nuna mini hanya. Na ga abin a matsayin ƙaddarawar Allah, wanda nai imanin cewa Shi Yake bayar da mulki yanda Ya ga dama, a lokacin da Ya ga dama. Tsare-tsarenSa ne ko yaushe a sama da namu.
“Duk da wannan cukumurɗa da ba ai tsammani ba, godiya ta ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya aminta da ni don samun wannan muhimmin matsayi ba zata gushe ba. Tafiyar ba ta ƙare a nan ba; na yi imani cewa, wannan wata matakala ce, alheri na nan zuwa. Shiri na na bautawa ƙasa ta Najeriya a kowanne yanayi da zan iya, ya ƙara ƙarfi sama da da.
“Ina so na tabbatarwa magoya baya na cewa, wannan ba shi ne ƙarshe ba, safiyar sabon zamani ce ta yi, ina kira gare mu gaba ɗaya da mu ci gaba da addu’a ga ƙasarmu, sannan mu goyi bayan shugaban ƙasarmu a ƙoƙarinsa na samar da Najeriya mai inganci. A tare gaba ɗaya, mu yunƙura mu ci gaba ƙarƙashin da’awarmu ta #WEBELIEVE,” in ji Maryam Shetty.