Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Masu Juyin Mulkin Nijar Zasu Yankewa Bazoum Hukuncin Cin Amanar Ƙasa

A ranar Lahadin da ta gabata ne da daddare, gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yi iƙirarin yankewa tsohon shugaban ƙasar da ta tunɓukar, Mohammed Bazoum hukuncin cin amanar ƙasa.

Sojojin sun kuma kushe hukuncin shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma bisa sanya takunkume-takunkume kan ƙasar ta Nijar.

Ƙungiyar Ci Gaban Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, ta sanya takunkume-takunkume kan Nijar saboda juyin mulkin da sojoji suka yi, sannan kuma ta yanke shawarar yin amfani da ƙarfin soja wajen kawar da sojojin daga mulkin ƙasar.

Shugabannin gwamnatin mulkin sojan a Nijar, sun yi alƙawarin yankewa Bazoum hukuncin cin amanar ƙasa tare da yin zagon ƙasa ga tsaron cikin gida da na wajen ƙasar Nijar, kamar yanda Kanal-Mejo Amadou Abdramane ya bayyana ta kafar talabijin.

Bazoum dai wanda ɗan shekara 63 ne a duniya, na hannun waɗanda suka yi masa juyin mulkin shi da iyalansa a gidan shugaban ƙasa da ke Niamey, babban birnin Ƙasar Nijar.

Akwai dai matsin lamba mai ƙarfi kan a saki Bazoum daga ɓangaren ƙasashen duniya da ƙungiyoyi da dama, musamman ma saboda yanayin da aka ce yana ciki na rashin ƙoshin lafiya, sai dai a ranar Asabar da ta gabata sojojin sun bari likitansa ya duba shi.

Sai dai likitan ya bayyana cewar, babu barazanar rashin lafiya a tattare da tsohon shugaban da kuma iyalinsa, kamar yanda sojojin suka rawaito shi yana faɗa.

Sojojin sun kuma koka kan takunkumin da aka sanyawa ƙasar, inda suka ce, hakan na wahalar da al’ummar ƙasar a ɓangaren samun magunguna, abinci da kuma wutar lantarki.