A yau Asabar, masu zaɓe da dama a yankin Tsakiyar Edo sun fito kwansu da kwarkwatarsu domin zaɓen gwamna duk da ruwan sama da aka tafka.
An fara kaɗa ƙuri’a da misalin ƙarfe 8:40 na safe a Makarantar Firamare ta Eguare, Ujiogba, Ƙaramar Hukumar Esan West, inda ake da rumfunan zaɓe guda uku.
Duk da ruwan saman, masu zaɓe sun yi layi don a tantance su da kuma yin zaɓe a lokaci guda.
A wasu rumfunan zaɓen, wasu masu zaɓen sun yi amfani da laima, yayin da wasu suka tsaya cikin ruwan saman.
Wani mai zaɓe, Samuel Samson, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, cewa an fara gudanar da zaɓen da misalin ƙarfe 8:30 na safe.
NAN