Rundunar Ƴansandan Jihar Jigawa ta tabbatar da kama wani matashi mai suna Muhammad Salisu ɗan shekara 20 daga unguwar Bakin Kasuwa, ƙaramar hukumar Gwaram, bisa zargin kashe mahaifinsa Salisu Abubakar, mai shekaru 57, ta hanyar kai masa farmaki da adda.
Rahoton da aka samu a safiyar Litinin, 5 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe goma na safe, ya bayyana cewa wanda ake zargin ya kai wa mahaifinsa farmaki har ya jikkata shi a kafaɗa, wuya da kirji.
WANI LABARIN: Mutane Da Dama Sun Mutu A Bauchi Bayan Wani Faɗa Tsakanin Ƴanbanga Da Ƴanbindiga
Kwamishinan ƴansanda na jihar, CP AT Abdullahi, ya bayar da umarnin miƙa binciken ga sashen binciken manyan laifuka na SCID Dutse domin zurfafa bincike.
SP Lawan Shiisu Adam, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ya ce “an garzaya da mamacin zuwa Asibitin Tarayya na Birnin Kudu domin kulawa da lafiyarsa, amma likita ya tabbatar da mutuwarsa.”
Bayan haka ne aka miƙa gawar ga ƴan’uwa domin gudanar da jana’iza kamar yadda addini ya tanada.
“An kama wanda ake zargin tare da ƙwato addar da ya yi amfani da ita wajen aikata laifin,” in ji SP Shiisu.
Rundunar ta ce bayan kammala bincike, za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu domin fuskantar hukuncin da doka ta tanada.