Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

MATSALAR KARANCIN FANSHO: Ba Kawai Ƴan Sanda Ba, Dukkan Ma’aikata Ne

Daga: Ahmed Ilallah

Bayan ɗaukar kwanaki, tsaffin ƴan sanda suna nuna suke shan wahalar rayuwa bayan sun yi ritaya a kafafen yaɗa labarai a jiya suka ƙaddamar da zangazangarsu ta kwanaki uku don neman kawo ƙarshen matsalar da suke ciki.

Yanayin da suka samu kansu na babban jami’in ɗansanda ya kan karɓi abin dai bai wuce naira miliyan 2 da rabi ba a matsayin gratuity da kuma abin da bai wuce dubu 30 ba a matsayin fansho.

Tabbas, wannan tsari dole ya zama tashin hankali ga duk wani ma’aikacin da yake karɓar albashin da ya tasamma dubu 300 a wata, a ce ya dawo yana karbar 30,000 a wata, ga yanayin da tattalin arziƙin Najeriya yake ciki.

To, wannnan fa ba iya kawai ƴan sanda ta shafa ba, harma da ma’aikatan gwamnati musamman na Tarayya da suke tsarin Haɗakar Fansho (Contributory Pension Scheme).

A Ina Matsalar Take?

Akwai matsaloli da dama da suka jawo wannan matsalar wanda zai yi wuyar gaske a wannan lokacin a shawo kanta har a kai yadda maaikatan da suka yi ritaya zasu gamsu da abin da ake biyan su na fansho.

Tsarin Pension Contributory Pension Scheme

A wannan tsarin na haɗakar fansho duk kuɗin da ma’aikaci ya tara da kuma gudunmawar da gwamnati ta saka masa, misali in har ya kai naira miliyan 10, za a bashi 25% na wannan kuɗi a matsayin Gratuity, sannan 75% zai kasance abun daza a na biyan sa a matsayin Fensho na wata-wata har inda hali yayi.

Duk da su ƴan sanda suna daga cikin jami’an tsaro mafiya muhimmanci a ƙasa, suna ganin gwamnatin tarayya bata musa adalci ba ta wajen mai da su tsohon tsarin fansho na PTDA kamar yadda aka yiwa sojoji da jami’an tsaron ɓoye.

A zahiri, ba kawai jami’an ƴan sanda ba, duk ma sauran ma’aikatan da suka yi ritaya ƙarƙashin wannan tsarin a cikin wannan wahalar suke.

Gazawar Tsarin PENCOM

Ko da yake a tarihin tsarin fansho ma a duniya, wanda a ka soma yinsa a Germany, tsarine na haɗakar adashe tsakanin ma’aikaci da hukumar da yake yiwa aiki.

Kuɗaɗen da aka tara ana biyan ma’aikaci gratuity da kuma fansho na watata da su.

Gwamantin Obasanjo a shekarar 2006 ta soma wannan tsarin don kawo ƙarshen matsalar fansho da ake fuskanta a ƙarƙashin tsohon tsarin.

WANI LABARIN: Yadda Gwamna Namadi Ke Kiyaye Daidaito Tsakanin Masarautun Jigawa

In zamu iya tunawa a wancan lokacin, tsoffin sojoji su kan cika titunan abuja suna neman a biya su haƙƙinsu bayan sun yi ritaya.

Tsarin biyan pension da gratuti a contributory pension ya ta’allaƙa ne a kan kuɗin da ma’aikaci da hukumar sa suka tara masa.

Zai yi wahala duk ma’aikacin da ya kwashe shekaru masu yawa yana aiki kafin 2006, ya zamanto kuɗaɗensa na fansho na da yawa.

Domin a baya albashin ma’aikatan ba shi da yawa, saboda tsarin da gwamnatin baya ta lissafa kuɗaɗen fanshon ne da mafi ƙarancin albashin da bai wuce naira 1,300 ko makamancin haka ba.

Kuɗaɗen da kasanya a asusunsu na fansho da wanda suka tara daga 2006 zuwa lokacin ritayarsu ne za a kacaccala musu tsakanin fansho da gratuti.

Haɗarin Da Ma’aikata Ke Faɗawa A Tsarin PENCOM

Na farko a kwai rashin kyakkyawan tsari da daidaito tsakanin albashin da ma’aikatan da kuma pension da za suna amsa bayan sun yi ritaya.

Misali ga tsoffin ƴan sandan, wani yana karɓar albashin da ya kai naira 300,000 yayin da yake aiki, amma yayin da ya yi ritaya zai kasance yana karɓar naira 30,000 a wata a matsayin pension sa na wata.

A wannan yanayi dole ne ma’aikatan su shiga wani yanayi na tashin hankali, saboda wannan tazara, tunda shi kansa albashin ma ba isa yake ba.

To wannan matsalar fa, ba kawai jami’an ƴan sandan wannan matsalar ta shafa ba, kusan dukkanin ma’aikatan da suke ƙarƙashin wannan tsarin.

Na biyu a kwai matsalar rashin ilmantar da ma’aikatan da zasu yi ritaya, a kan rayuwar da zasu sami kansu bayan sun ajiye aiki.

Ya kamata ita kanta dokar da ta kafa Contributory Pension Scheme ɗin an mata gyara, musamman a kan kason da za a na ware wa don sakawa a asusun ma’aikatan.

alhajilallah@gmail.com