Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ministan Ayyuka Ya Mayar Da Zazzafan Maratani Ga Kwankwaso, Ya Kuma Buƙaci Ya Ba Wa Tinubu Haƙuri

Ministan Ayyuka, David Umahi, ya buƙaci tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da ya janye kalamansa tare da ba Shugaba Bola Tinubu haƙuri kan zargin cewa gwamnatin tarayya na fifita yankin Kudu wajen ayyukan raya ƙasa.

A wata sanarwa da ya fitar kuma mai ɗauke da sunan mai ba shugaban ƙasa shawara kan dabarun yaɗa labarai, Bayo Onanuga, Umahi ya ce kalaman Kwankwaso na iya raba kan al’umma kuma ba su dace da gaskiyar abubuwan da ke faruwa ba.

Ya ce, “Ɗan’uwa na Kwankwaso, za ka ba wa shugaban ƙasa haƙuri, kuma nauyin janye kalamanka ya hau kanka.”

Umahi ya bayyana wasu daga cikin manyan ayyukan da ake yi a Arewa, kamar hanyar Sokoto-Badagry mai tsawon kilomita 1,068 da kuma gyaran hanyar Akwanga-Jos-Bauchi-Gombe mai tsawon kilomita 439.

Ya jaddada cewa a cikin manyan ayyuka huɗu da gwamnati ke aiwatarwa, Arewa ce ke da kaso 52 cikin ɗari, yayin da Kudu ke da kaso 48 cikin ɗari.

WANI LABARI: Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Faɗawa Gwamnoni Magana Kan Kuɗaɗen Da Suke Samu Daga Asusun Tarayya

“Ina mamakin yadda ake ta magana kan hanyar gaɓar tekun Legas zuwa Calabar, amma ba sa ambato ayyukan da ake yi a Kebbi da Sokoto da sauran sassan Arewa,” in ji shi.

Kwankwaso dai a wani jawabi da ya yi a Kano ya zargi gwamnatin Tinubu da karkatar da akasarin kasafin kuɗin ƙasa zuwa Kudu, yana mai cewa hakan na ƙara tsananta matsalolin tsaro da talauci a Arewa.

“Wasu daga cikin matsalolin da muke fuskanta – kamar rashin tsaro da talauci – suna da alaƙa da rashin isassun albarkatu da kuma ɓarna ga kaɗan da muke samu,” in ji Kwankwaso.

Umahi ya ce irin waɗannan kalaman na nuni da yunƙurin siyasa ne kawai, domin neman amfani da sunan marigayi Shugaba Muhammadu Buhari don samun tasiri a Arewa.