Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ministan Tsaro Ya Ƙalubalanci Yin Taron Ƙasa Don Inganta Tsaro, Ya Yi Kiran Sauyin Dabaru

Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na buƙatar sauyin dabarun yaƙi da rashin tsaro, maimakon ƙara yin taro ko tarukan ƙasa kan matsalar.

Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai a Abuja, yayin da Majalisar Dattawa ke shirin gudanar da taron tsaro na kwana biyu domin tattauna hanyoyin daƙile yawaitar kashe-kashe da rikice-rikicen da ke addabar ƙasa.

A cewar Badaru, “Taro na iya samar da shawarwari, amma dabaru su ne mafita. Bayan taro, sai a tsara dabaru kuma shugabannin runduna su fitar da umarni bisa waɗannan dabaru.”

Ya ce ba gaskiya ba ne cewa ƴan ta’adda na da makamai fiye da na dakarun Najeriya, yana mai cewa “mu ne muke da makaman zamani da drones masu inganci.”

WANI LABARIN: Wata Rundunar Ƴansanda Ta Cafke Matsafa 95 Da Ƙwato Makamai Da Dama Cikin Wada Ɗaya

Ministan ya ce wannan ba ya kama da yaƙin gargajiya, domin ƴan ta’addan na bin hanya irin ta gwagwarmaya ta amfani da bayanai daga cikin jama’a domin kai farmaki ba tare da an yi tsammani ba.

A wani ɓangare kuma, ya bayyana cewa yanzu haka kamfanoni 10 daga cikin 53 da ke ƙarƙashin cibiyar masana’antar tsaro sun fara samar da jirage marassa matuƙa, sassan jirgin sama, hular kariya da rigunan tsaro.

“Muna fatan kashi 20 cikin 100 na kamfanonin su fara aiki nan da ƙarshen shekara, sannan a fara fitar da kayan da suka samar zuwa ƙasashen waje a shekarar 2026,” in ji Badaru.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da shirin farfaɗo da wasu sassa na kamfanin Ajaokuta Steel domin samar da kayan aikin soja a cikin gida, yayin da rahoton PUNCH ke nuna cewa harin da aka kai Benue da Borno ya yi sanadin mutuwar wani hafsan soja da jigon jam’iyyar APC.