Majalisar Dinkin Duniya ta ce tsawa ta hallaka mutuane 10 bayan mamakon ruwan sama da kuma afkuwar wata mahaukaciyar guguwa a Mozambique.
Ofishin bayar da agaji na Majalissar Dinkin Duniya ta ƙara bayar da sanar cewa wasu mutum 11 sun mutu a Madagascar, inda gidaje sama da 3,300 suka lalace a ranar Lahadi lokacin da guguwar ta sake afkawa tsibirin.
WANI LABARIN: Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Jawo Mutuwar Mutane Da Dama A Kwande, Jihar Benue
Masu lura da yanayi, sun yi hasashen cewa mahaukaciyar guguwar za ta afkawa yankin tsakiya da kuma arewacin Mozambique a makon nan.
Guguwar ta kasance ɗaya daga cikin mafi daɗewa a cikin gwamman shekaru, inda ya tsallake ɗaukacin tekun Indiya daga bakin tekun Indonesia zuwa kudancin Afirka.
BBC