Daga: Ahmed Ilallah
Shin ya.za a kira wannan ciniki tsakaninn Kungiyar Kwadago da Gwamnatin Tarayya?
Shin Gwamnati zata iya biyan N615,000 ko Yan Kwadago zasu aminta da tayin N48,000 din a ka yi musu?
Wannan mugun tayi na Gwamnatin tarayya, kamar ya biyo bayan mugun farashin da yan kwadago suke ganin sun sanya musu ne.
Saboda ko a yanzu ma fa, mafi karancin albashi a Gwamnatin Tarayya ya fi N48,000.
In zamu iya tunawa, daga mafi karancin albashi na N30,000, tsohuwar Gwamnatin Buhari ta karawa wasu ma’aikatan kashi 40% da ta kira Peculiar Allowance, ita ma Gwamnatin Tinubu a 1 ga wannan watan ta sake kara kashi 25% da 35% ga ma’aikatan.
In a kayi lissafi, yanzu karacin albashi a Gwamnatin Tarayya ya kai N49,200.
Kari ga wannan fa, Jahohin Edo da Lagos, mafi karancin albashin su N70,000 ne.
Soma tayi da N48,000 da Gwamnati tayi, kamar maida bakar magana ne ga mugun farashin Yan Kwadago na N615,000.
Duk da kasancewar Kasar Nijeriya ce mafi girman tattalin arziki a nahiyar Africa, amma bata iya biyan Ma’aikatan ta albashin da a kalla za su sami kyakkyawar rayuwa.
Ko da kasashe irin su South Africa, Egypt, Kenya, Tunisia da arzikin su bai kai na Nijeriya ba, su na
biyan yan kasar su albashi mai kyau.
Babbar matsalar arzikin Nijeriya, shine gazawar shugabancin da zai sanya yawa da girman arziki ya malalo zuwa ga al’umar kasar, don samin ingantacciyar rayuwa.
Ya kamata a ce a yau Nijeriya na iya yin Kasafin Kudin da ya kai N80 Tiriliyan zuwa sama,
Amma saboda rashin tsarin tara kudaden shigowa ga gwamnatin da tsananin cin hanci da rashawa da cin amanar gwamnati, yan kasar suka samu kan su a matalauciyar rayuwa.
A wannan fadan karshe tsakanin Yan Kwadago da.Gwamnatin Tarayya na samun sasanto a kan mafi karancin albashi, zai yi wuya ko wane bangare ya samu abin da yake so.
Kowa ya san gaskiya da abin da zai iyu, za a kawo farashi na gaskiya da kuma tayi na gaskiya.
alhajilallah@gmail.com