Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Najeriya Zata Karɓi Bashin Naira Tiriliyan 3.2 Daga Bankin Duniya A Ranar 13 Ga Yuni

Gwamnatin Tarayya ta shirya domin karɓar sabon bashi daga Bankin Duniya mai yawan adadin dala biliyan 2.25 daidai da naira tiriliyan 3.2 a ranar 13 ga watan Yuni, 2024.

Najeriyar zata karɓi waɗannan maƙudan kuɗaɗe ne saboda wasu manyan aiyuka guda biyu, da suka haɗa da Shirin Tsare-tsaren Daidaita Tattalin Arziƙin Najeriya domin Samun Ingantaccen Cigaba wanda zai laƙume dala biliyan 1.5 na bashin.

Aiki na biyu kuma shine Shirin Samar da Kayan Aiki na NG Accelerating Resource Mobilization Reforms Programme-for-Results, wanda zai laƙume dala miliyan 750 na bashin.

Saboda samun amincewar masu bayar da wannan bashin dai, akwai yiwuwar Najeriya zata dawo da harajin amfani da waya wanda aka dakatar a baya da kuma wasu haraje-haraje da suka shafi harkar hada-hadar kuɗi a bankuna.

Tun a watan da ya gabata ne, Ministan Kuɗi na Najeriya, Wale Edun, a wani zaman tattaunawa tsakanin Asusun Bayar da Lamuni na Duniya da Bankin Duniya ya bayyana cewar, Najeriya ta cika dukkan ƙa’idojin da ake buƙata domin karɓar bashin na dala biliyan 2.25 a kan kuɗin ruwa kashi ɗaya cikin ɗari.