Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

NANS Ta Roƙi Gwamnati Da Ta Janye Sokewar Da Tai Wa Digirin Benin Da Togo

Shugabannin Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya ta NANS a yankin kudu maso yamma sun roƙi gwamnatin tarayya da ta sake nazari kan soke shaidar karatun digiri daga manyan makarantu na ƙasar Benin da Togo.

A cikin wata sanarwa da Shugaban Reshen Ƙungiyar, Kwamared Alao John, Sakataren Reshen Ƙungiyar, Kwamared Sanni Sulaimon Olamide, da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Reshen, Kwamared Bamigboye Peter Oluwadamilola suka fitar, ƙungiyar ta ce tana magana kan lamarin ne saboda yawan ɗaliban Najeriya da abin ya shafa.

Sun bayyana cewa, soke digirin ya haifar da damuwa ga ɗalibai sama da 22,000 a Najeriya, lamarin da ke barazanar kawo rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar.

Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta lura da ƙudirin shugaban ƙasa na ganin ba ɗalibin Najeriya da zai asarar karatunsa, yana mai cewa waɗanda suka kashe dukiyarsu wajen karatu a ƙasashen waje sun tsinci kansu cikin damuwa game da makomarsu bayan jin wannan labarin.

Sun amince cewa akwai damuwa kan karuwar makarantu marasa inganci da kuma buƙatar dakile almundahana a harkar ilimi, amma soke digirin ba tare da yin cikakken bincike ba, musamman waɗanda aka amince da su a baya, abu ne na rashin adalci da nuna bambanci.

Ƙungiyar ta ce ta na ganin gwamnati ya kamata ta duba batun tare da haɗin gwiwar hukumomin ilimi na yankin don tabbatar da cika ƙa’idojin ilimi, maimakon soke digirin gaba ɗaya.

A ƙarshe, ƙungiyar ta yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da kare haƙƙin ɗalibai tare da samar da mafita don inganta zaman lafiya da ci gaban ƙasa.