Ƙungiyar Al’ummar Inyamurai (Igbo) ta Ohanaeze Ndigbo ta koka kan naɗin iya ministoci biyar daga yankin Kudu Maso Gabas da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi.
Shugaban Ohanaeze, Emmanuel Iwuanyanwu ya ce, bai wa yankin Kudu Maso Gabas iya gurabe biyar a ministocin Tinubu, nuna rashin gaskiya da rashin adalci ne.
A wata sanarwa a jiya Alhamis, Iwuanyanwu ya ce, yayin da sauran yankuna suke da mafi ƙarancin jihohi 6, yankin Kudu Maso Gabas yana da iya jihohi biyar ne kacal.
Ya bayyana cewa, a yanzu abun da Ohanaeze ke buƙata shine, “adalci, gaskiya, da daidaito ga kowacce ƙabila a Najeriya ciki har da Igbo.
Ya ce, in za a iya tunawa, ƙirƙirar yankuna shida a Najeriya aikin gwamnatocin soja ne, inda ya ce, dukkan wani ɗan Najeriya mai adalci ya san cewar babu hannun Igbo a cikin aikin rabon.

Iwuanyanwu ya ce, wannan ne dalilin da ya sa aka bai wa yankin Kudu Maso Gabas iya jihohi biyar, yayin da sauran jihohi suka sami mafi ƙaranci, jiha shida.
Ya bayyana cewa, wannan yanayi ya jefa al’ummar yankin Kudu Maso Gabas cikin mawuyacin hali a siyasance, a ɓangaren tattalin arziƙi da kuma ɓangaren zamantakewa.
Ya ce, hakan ya rage musu ƙarfi a siyasance, inda suke da sanatoci mafiya ƙaranci, da ƴan majalissar wakilai ƴan kaɗan, da gwamnoni biyar kacal da kuma ƴan majalissar jihohi da na ƙananan hukumomi mafiya ƙaranci.
Iwuanyanwu ya ƙara da cewa, ana tauye yankin Kudu Maso Gabas a rabon kuɗaɗen ƙasa da rabon muƙaman gwamnati da sauran kasafin arziƙin ƙasa da ake yi.
Ya ce suna sane da cewar, wannan yanayi bai fara a wannan gwamnatin ba, amma suna roƙon Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da ya temaka musu wajen magance waɗannan matsaloli domin tabbatar da adalci, daidaito da kuma aikata gaskiya a Najeriya.