Asusun Lamunin Dalibai na Ƙasa (NELFUND) ya ce ya riga ya raba naira biliyan 86 don tallafa wa ɗalibai 449,000 cikin buƙatu 735,000 da aka samu zuwa yau, kamar yadda Akintunde Sawyerr ya bayyana a shirin Sunrise Daily na Channels Television a yau Juma’a.
A cewarsa, “a safiyar yau, ɗalibai 742,000 sun yi rajista a shafinmu kuma an tantance su a matsayin masu iya nema, kuma daga ciki ɗalibai 735,000 sun kammala shigar da buƙatunsu.”
Sawyerr ya ce an biya naira biliyan 47 ga jami’o’i, kwalejojin ilimi da polytechnics 218 a matsayin kuɗin rijistar ɗalibai, sannan an biya naira biliyan 38 a matsayin tallafin kuɗin kai-da-kai ga ɗalibai, inda ya ƙara da cewa, “a jimlace, mun rarraba naira biliyan 86.”
Game da saurin aiwatar da shirin ba wa ɗalibai kuɗaɗen, ya jaddada cewa lokacin samun lamunin “yana tsakanin kwanaki 30 zuwa 45 idan mai nema ya cika dukkan sharudda,” tare da bayanin cewa ba sa biyan kowa a kan wani wa’adi na musamman.
Ya ce tsarin yana tura bayanan zuwa makarantar ɗalibi domin tantance sunansa, shirin karatu da kuɗin karatu, kuma “sai bayan mun karɓi tabbaci da sa hannu daga makaranta muke ci gaba da aiwatarwa, kuma wannan aikin na cikin gida kan ɗauki makonni biyu zuwa uku.”
Yayin da ya amince da damuwar jama’a kan gaskiya da bin doka, ya ce “sarrafa kuɗin jama’a na ƙarƙashin tsarin tsantseni, dole ne a kasance da alhakin aiwatarwa a kowane mataki,” a dai dai lokacin da ICPC ke binciken zargin naira biliyan 71 da ba a iya fayyace su ba, da kuma zargin cire kuɗi ba bisa ka’ida daga kuɗin makarantu, abin da NELFUND ta musanta.
Haka kuma, Majalisar Wakilai ta ƙaddamar da bincike kan yiwuwar saɓawa Dokar Lamunin Ɗalibai, alhali NELFUND ta ce buƙatar shiga shiga shirin daga ɗalibai na ƙaruwa “kimanin ɗalibai 3,000 zuwa 3,500 a rana,” abin da ke nuna shirin na ci gaba da faɗaɗa.