Ƙungiyar ci gaban al’umma ta Next Jigawa ta yi kira ga gwamnatin jihar da cire takunkumi kan ɗiban ma’aikata tare ɗiban ma’aikatan da zasu cike guraben aikin da ake da su a jihar.
Shugaban Ƙungiyar, Farfesa Haruna Usman ne ya yi kiran, lokacin da yake ganawa da ƴan jaridu a ɗankin taro na gidan talabijin na Jigawa wato JTV a jiya Alhamis.
Ya bayyana cewa, ƙarancin masu gudanar da aikin gwamnati da dakatar da ɗaukar sabbin ma’aikata da kuma ƙarancin bayar da horo ga ƴan waɗanda ake da su na kan gaba cikin ƙalubalen da Jihar Jigawa ke fuskanta.
Farfesa Usman ya ƙara da cewa, akwai matuƙar zagwanyewar ƙwararrun ma’aikata a jihar, wadda ta samo asali daga ritayar da dama daga cikinsu suka yi da kuma rasuwa, ga kuma uwa-uba rashin cike gurabensu da ƙwararru da kuma rashin bayar da horarwa ga waɗanda ake da su.
Labari Mai Alaƙa: Haɗakar Kungiyoyin Ci Gaban Al’umma Ta Jigawa Ta Zabi Sabbin Shugabanni
Shugaban na Next Jigawa ya nuna cewa, samun nasarar magance wannan matsalar a Jihar Jigawa ba ƙaramin gagarumin ci gaba zai haifar ga rayuwar al’ummar jihar ba.
Farfesan ya baiwa gwamnatin jihar shawara kan ta samar da kwamiti na musamman da zai duba yanayin da ake ciki tare da lura da buƙatun jihar game da yawan ma’aikata da fannonin da ake buƙata domin samar da ingantacciyar nasara.
Ya kuma shawarci gwamnatin da ta haɗa guiwa da kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyoyin samar da ci gaba, domin magance matsalar ma’aikatan, sannan kuma ta shigar da manyan makarantun jihar ciki, domin samar da ƙwarewar da ake buƙata wajen cike guraben da ake da su.
A ƙarshe, Farfesa Usman ya ƙara kira ga gwamnatin jihar da ta samar da hanyoyin magance matsalolin rashin ɗa’ar ma’aikata tare da gina ƙarin gidaje a birnin jihar, Dutse domin killace ma’aikata a guraren da zasu gudanar da aiyukansu cikin nasara.
Ana dai ci gaba da ƙorafe-ƙorafen kan ƙarancin ma’aikata a ɓangarorin aiyukan gwamnati daban-daban da ke Jihar Jigawa, wanda ya samo asali daga rasuwa da kuma ritayar ma’aikata da dama na tsawon lokaci ba tare da ana cike gurabensu ba.
