Shugabancin Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, ya bijirewa zaman da Ministan Ƙwadago da Ɗaukar Ma’aikata, Simon Lalong ya kira domin dakatar da yajin aikin kwanaki biyu da NLC ta fara a yau Talata.
A zaman da aka gudanar jiya Litinin da yamma, iya shugabancin Ƙungiyar Ƴankasuwa, TUC, ƙarƙashin shugabanta, Festus Osifo tare da sauran shugabanni na ƙasa suka halarta.
Da dama daga cikin ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin NLC da ƙungiyoyi masu zaman kansu sun nuna shiryarwarsu game da yajin aikin gargaɗin na kwana biyu wanda NLC ta fara jagoranta a yau.
Ƙungiyoyin sun haɗa da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU; Ƙungiyar Malaman Makarantun Kimiya da Fasaha, ASUP; ƙungiyoyin ma’aikatan da malamai na jami’o’i; Ƙungiyar Haɗin Kan Bankuna; da kuma Ma’aikatan Ɓangaren Inshora da Hukumomin Hada-hadar Kuɗaɗe, NUBIFIE.
KARANTA WANNAN: Ɗalibai Da Fusatattun Matasa Na Shirin Yin Zanga-Zangar Tarzoma Kan Matsatsin Da Ake Ciki A Najeriya, In Ji DSS
Sauran sun haɗa Ƙungiyar Ma’aikatan Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa, NUATE da kuma Ƙungiyar Matuƙan Jiragen Sama da Injiniyoyin Jiragen Sama ta Ƙasa, NAAPE.
Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ne, NLC ta ayyana cewar ma’aikata a duk faɗin Najeriya zasu shiga yajin aikin gargaɗi na kwanaki biyu daga ranar 5 ga watan Satumba kan matsatsin rayuwar da ƴan Najeriya ke ciki, wanda kuma NLC ke zargin Gwamnatin Tarayya da yin biris da yanayin.
To amma a zaman tattaunawar da aka yi tsakanin Ministan Ƙwadago, Lalong da Ƙungiyar TUC a jiya da yamma, Gwamnatin Tarayya ta buƙaci a ba ta sati biyu kafin ta yi wani abu game da buƙatun ƙungiyoyin ƙwadagon.